Wani matashi da ya kitsa sace yayarsa a kan kudin da ta bashi Naira miliyan daya da dubu dari hudu ya shiga hannu.
Runduna ta musamman mai yaki da ayyukan ta’addanci da satar mutane, wadda Shugaban ’Yan Sanda ya kafa (IRT), ce ta cafke matashin, wanda mazaunin unguwar Magumai ne a yankin Tukur Tukur ta Karamar Hukumar Zariya a jihar Kaduna.
- Yadda ’yan bindiga suka tare a makarantun Zamfara
- Amarya ta kashe ango kwana biyu bayan daurin aure a Adamawa
Matashin, mai shekara 35, ya shaida wa runduar cewa ya sa an sace yayar tasa ce saboda kudin da ta ba shi Naira miliyan daya da dubu dari hudu ya juya ya yi kasuwanci.
Bayan ya shiga hannu, matashin ya ce ya shi ne ya shirya da wasu kwararrun masu satar mutane suka yi garkuwa da shi da yayar tasa.
A cewarsa, suna kuma noma a kauyen Kugu da ke gundumar Dutsen Abba, yankin da ya yi kaurin suna wajen satar mutane domin karbar kudin fansa, kuma a nan ne ya ya hadu da ’yan ta’addar.
A bayanansa, ya ce ya shirya yadda za a sace shi tare da yayar tasa a kauyen domin idan ita kadai aka sace tana iya zargin cewa da shi aka hada baki.
“Bayan an yi garkuwa da ni da ita an ajiye mu a wuri daya, daga baya sai shi aka dauke ni cewa za a je a kashe ni, amma sai aka sake ni, tun da dama haka muka tsara, shi ne daga baya aka sako ni ita kuma aka ci gaba da tsare ta.
“Kuma ga shi yanzu ita yayar tawa tana can hannunsu ni kuma ga shi asirina ya tuno,” inji shi.
Yanzu haka yana hannun hukumar domin gano inda yar tashi take.
Yankin Zariya dai ya yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane, inda a lokuta da dama aka kama wasu da suka hada baki da masu garkuwa suka ce danginsu.