Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kuros Riba, ta kama wani matashi mai suna Edmund Sampsun, mai shekara 29, kan zargin kashe mahaifiyarsa domin yin tsafi da sassan jikinta.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Batriko da ke Ƙaramar Hukumar Boki a Jihar.
- DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato
- Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani
Rahotanni sun bayyana cewa matashin ya amsa laifin ba tare da tilasta masa ba.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Irene Ugbo, ta tabbatar da kama matashin, wanda ke tsare.
Ta ce matashin ya datse kan mahaifiyarsa sannan ya yi yunƙurin amfani da sassan jikinta domin yin tsafi.
SP Ugbo, ta ƙara da cewa an kama matashin ne a ranar 25 ga watan Disamba, 2024, bayan jami’an tsaro sun yi masa kwanton-ɓauna.
Bayan kashe mahaifiyarsa, ya yi yunƙurin tserewa, amma aka gano maɓoyarsa kuma aka kama shi.
Lamarin ya tayar da hankalin jama’ar ƙauyen, inda suka yi wa iyalanta ta’aziyya kan wannan mummunan al’amari.
Kakakin ta ce: “Matashin yana hannunmu kuma ana ci gaba da masa tambayoyi. Da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da shi a gaban kotu.”