Wani matashi mai suna Success ya shiga hannu kan zargin kashe mahaifinsa a yankin Amukpe da ke Ƙaramar Hukumar Sapele a Jihar Delta.
Bayanai sun ce matashin mai kimanin shekaru 23 ya kashe mahaifin nasa da adda sanadiyyar taƙaddama kan kuɗin da ba su wuce Naira dubu biyar ba.
- Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana
- IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur
Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne bayan mahaifin ya yi wa ɗan nasa ƙememe wanda ya nemi kuɗin a wurinsa.
Wani maƙwabcinsu da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce irin wannan harzuka da Success ya yi ba ita farau ba musamman a duk lokacin da ya yi shaye-shayensa na kayan maye.
Maƙwabcin ya ce Success ya sassari mahaifin nasa da adda wanda aka yi gaggawar kai shi asibiti inda a nan ya ce ga garinku nan.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Delta, Bright Edafe wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce yanzu haka matashin yana hannu.
Ya buƙaci mazauna da su riƙa gaggauta kai rahoton makamancin wannan lamari ga mahukunta tare da jaddada muhimmanci yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.