Ana zargin wani matashi mai suna Ufuoama Umurie ya kashe mahaifinsa a Unguwar Okpare da ke Ƙaramar Hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta, ranar Laraba.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an tsinci gawar mahaifin mai suna Rabaran Isaac Umurie, wanda ɗaya ne daga cikin limaman cocin St. John’s Anglican da ke Okpare-Olomu a safiyar wannan Larabar.
- Majalisa ta kori kudurin hana hafsoshin tsaro karkatar da kudade
- An kama shugaban ’yan banga da sassan jikin dan Adam
Bayanai sun ce tun farko lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na tsakar dare, inda wanda ake zargin ya kori mahaifiyarsa a lokacin da take ƙoƙarin ceto rayuwar mijinta amma ita kanta da ƙyar ta tsira.
Ufuoma, wanda a halin yanzu yana hannun ‘yan sanda, an ce ya yi amfani da laujen yankar ciyawa ya yanka mahaifinsa sannan ya sassare shi a sassan jikinsa.
Rahotanni sun ce matashin ya yi wa mahaifinsa wannan aika-aikar ce a lokacin da yake barci kafin maƙwabta da mabiya cocin su su kawo dauki.
Duk da cewa har yanzu ba a gano abin da ya haddasa faruwar lamarin ba, wasu mazauna unguwar yankin sun yi zargin cewa Ufuoma yana fama da taɓin hankali, kuma wannan ne karo na biyu da ya kai wa mahaifin nasa hari.