Wani da ake zargin barawon waya ne ya kashe wata dalibar a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Samaru, Zariya
Wata majiya mai tushe wadda ke cikin masu bincike a kan lamarin ta shaida wa Aminiya cewa a ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe 10:00 na dare ne aka tsinci gawar dalibar da aka yi wa kisan gillar mai suna Deborah Precious Asso da ke shekarar farko a sashin karatun likitan dabbobi da ke Jami’ar Ahmadu Bello, a Samaru Zariya.
Majiyar ta ce an tsinci gawar Deborah ce a yashe a wani layi mai suna Nuhu Bayero da ke da lamba 147 a Rukunin Gidajen Ma’aikatan Jami’ar na (F), kuma wadanda suka kashe dalibar sun tafi da wayoyinta na hannu samfurin Sonny Edpress da ke lambar kira ta 081-24129772, sai kuma waya kirar Techno mai lambar kira 070-32964514, kuma an same ta da alamar rauni a jikinta.
Aminiya ta tuntubi Daraktan Labarai na Jami’ar, Adamu Muhammed, kan lamarin inda ya ce yana da masaniya sai dai mai kula da jin dadin dalibai bai riga ya yi masa bayani a kai sosai ba.
Wakilinmu ya tuntubi Shugaban Sashin Kula da Harkoki da Walwalar dalibai na Jami’ar Farfesa Yahaya Yunusa Bambale ta waya har sau biyu amma bai dauki wayar ba, kuma ya tura masa sakon tes nan ma bai ba shi amsa ba.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mukhtar Hussaini Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace, lamarin ya faru ne ranar Juma’a da daddare, kuma washegari Asabar aka sanar da su, su da hukumar tsaron makaranta suka shiga bincike. “Kuma mun fara samun nasara don mu kama wanda ake zargi da kisan a wuraren PZ, mai suna Magaji Nasiru mai kimanin shekara 40, kuma mun samu waya daya daga cikin wayoyin biyu na marigayiyar a hannunsa, tare da kama wani abokinsa da ya sayar masa da daya wayar. Wanda ake zargin ya dauki dalibar ce tare da wata kawarta daliba a jami’ar a inda ya sauke kawar a inda za ta sauka ya wuce da marigayiyar inda ta za ta je. Bayan ya amsa cewa shi ne ya kashe dalibar, kuma kawarta da ya dauko su tare ita ma ta shaida shi cewa shi ne ya dauke su don haka muna ci gaba da da tattara bayanai da kuma neman daya wayar da ya sayar kafin mu dauki mataki na gaba,” inji shi.
Wanda ake zargin da ke zaune da iyalinsa a Unguwar Ban Zazzau a Zariya, yana sayar da kayan babura da kwancen wayoyi ne a Layin Siliki, daura da Albarka Silima a Tudun Wada Zariya. Ana zargin idan dare ya yi ne yakan zaga domin gudanar da muguwar sana’arsa ta fashi da kwacen wayoyin jama’a.