Wani matashi dan shekara 19 ya daba wa budurwarsa wuka ya hallaka ta a kan kudi Naira dubu biyar a Jihar Bauchi.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammad Wakil, ya bayyana cewa tuni ’yan sanda sun kama wanda ake zargin.
Wakil ya ce, “abin ya faru ne a lokacin da wanda aka kashen ta bukaci a biya ta Naira 5000 da take bin (wanda ake zargin) bashi, a kan harkokin da suka yi a baya.
“Ana cikin haka sai gardama mai zafi ta shiga tsakaninsu har ta kaiga ya daba mata wuka, ta samu mummunan rauni wanda ya kai ga mutuwarta.”
Wakil ya bayyana cewa a ranar 18 ga watan Disamba, 2023 jami’an tsaro suka kama shi a unguwar Sabon Layi Kano Road Bauchi bisa zargin kashe Emmanuella Ande.
- Kotun Koli ta sanya lokacin yanke hukunci kan Zaben Gwamnan Kano
- Tinubu ya dawo da shirin ciyar da dalibai a makarantu
A cewarsa, an kama shi ne sakamakon kiran da wani mutum ya yi musu cewa wanda ake zargin ya shiga dakin otal da ke Bayan Gari, ya daba wa budurwarsa wuka a kirjinta.
“Jama’ar sun yi yunkurin ceto ta, inda suka balle kofar dakin, inda shi kuma ya daba wa wani Zaharaddeen Adamu wuka a hannun hagunsa,” in ji shi.
Wakil ya ce, ’yan sanda sun hanzarta kai dauki, inda suka ceto wanda ake zargin, aka kai ta asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) Bauchi inda likita ya tabbatar da rasuwar ta, kuma aka ajiye gawar a dakin ajiyar gawa.
Hakazalika an kai Zaharadeen an yi masa magani a asibitin ’yan sanda, aka sallame shi, wanda ake zargin kuma a halin yanzu ana ci gaba da bincike.