✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasan kungiyar asiri sun halaka matashi a Kalaba

Wasu matasa da ake kyautata za to ’yan kungiyar asiri ne, da suka zo cikin karamar mota sun bude wa wani matashi mai suna Saifullahi…

Wasu matasa da ake kyautata za to ’yan kungiyar asiri ne, da suka zo cikin karamar mota sun bude wa wani matashi mai suna Saifullahi Muhammad wuta, yayin da yake bakin sana’arsa ta sayar da nama a unguwar Essien Town da ke birnin Kalaba.
dan uwan mamacin, Idris Muhammad ya shaida wa Aminiya yadda ’yan ta’addar suka far masu lokacin da suke tsaka da cin kasuwarsu ta sayar da nama a wannan unguwa. Ya ce: “Saifullahi mutumin garin Unguwar Liman da ke karamar Hukumar Kibiya Jihar Kano ne, mun dade da shi muna sana’ar sayar da nama tare, daki daya ma muke tare. Abin da ya faru shi ne, muna zaune wurin mai shayi sai muka ga wata farar mota kirar Audi ta dan faka a gefe, sai wasu daga ciki suka fita suka gangara kasa suka samu mutanenmu a zaune. Farko sai suka kama su da kokawa, wasu daga cikinsu suka zaro adduna, sai suka taso da gudu suka yo kanmu. Ni ina wurin mai shayi na ga sun rugo mana, sai nake tambayarsu daga ina kuke haka kuke gudu?” Inji shi.
dan uwan nasa ya ci gaba da bayyana yadda wannan kisan gilla ya wakana. “Sai na ce wannan ai bai kamata ba ma ku rika gudu. Idan ma ’yan iska ne, kamata ya yi ku tsaya ku ga hanzarinsu tun da mun fi su yawa. Ashe hakan ke da wuya, har sun far wa Saifullahi da sara da adduna tun daga gadon bayansa zuwa kansa, sun yi masa illa, sun sassara shi a gadon bayansa da kuma cikinsa.”
Shi kuwa Alhaji Ali Abdullahi, wani dan kasuwa da yake tofa albarkacin bakinsa game da lamarin, ya shaida wa wakilinmu shawararsa ce ga ’yan kasuwa musamman mahauta da ke tafiya cikin gari talla sai dare ya yi su dawo. “Shawarar da zan ba su ita ce, tun da sun ga ga yadda gari ya koma, bai kamata ba su rika kaiwa dare misalin karfe sha daya koma fiye, su dawo daga kasuwa ba; kamata ya yi su rika baro wuraren tallarsu don kauce wa kaddara irin wannan.”
Haka kuma wakilinmu ya ji ta bakin Alhaji Salisu Abba Lawal, Sarkin Hausawan Kalaba game da matakin da aka dauka. “Mun sanar wa da hukumar ’yan sanda kuma sun ce za su dauki mataki kuma kisan nan ba shi da nasaba da kabilanci ko addini. Ka san wasu ’yan iska ne kawai suke hana jama’a sakewa.” Ya kara da kira ga ’yan Arewa mazauna Kurosriba da kuma Kalaba babban birnin jihar, su hada kai kuma da zarar sun ji ana fara wani abu daban na rashin kwanciyar hankali, su yi taka-tsan-tsan don gudun fadawa rikici ko ’yan iska masu cin zarafin jama’a babu wani dalili; sannan su daina dadewa wurin sana’arsu har zuwa na tsawon wani lokaci.