✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasan Kano ta Arewa sun amince da wakilcin sanatansu

Dubban matasan yankin Kano ta Arewa da suka fito daga kananan hukumomi 13 na mazabar ne suka gudanar da wani gangamin taro na hadin gwiwa…

Dubban matasan yankin Kano ta Arewa da suka fito daga kananan hukumomi 13 na mazabar ne suka gudanar da wani gangamin taro na hadin gwiwa tsakanin ‘ya’yan APC Gandujiyya da kuma sauran kungiyoyi daban-daban musamman masu amfani da yanar gizo wajen sadarwa domin nuna amincewarsu da goyon bayansu ga wakilcin Sanata Barau Jibrin, inda suka sha alwashin sake kada masa kuri’arsu a 2019.

Shugaban hadakar mai taken ‘Sanata Barau Jibrin an samu riba’ Kwamared Kamaluddeen Ado Sidi Zogachi ya bayyana cewa duba da irin dimbin nasarorin da yankin ya samu a shekaru biyu na mulkin sanatan ya zama wajibi a gare su fito kwansu da kwarkwatarsu domin sake zaben Sanata Barau duba da kokarinsa na bunkasa rayuwar al’ummar yankin.

A cewar Kwamared Kamaludden Sanatan nasu yana bayar da tallafin karatu ga daliban yanki haka kuma ba wa wasu da yawa daga cikinsu tallafin jari inda suka fara sana’o’i.. “Baya ga wannan, Sanata Barau ya samar wa da matasan yankin maza da mata aikin yi a matakin jiha da gwamnatin tarayya sama da 200. 

Haka kuma ya raba motoci ga kungiyar daliban kananan hukumomin Kano ta Arewa. Haka kuma ko a lokacin azumi da ya gabata Sanata Barau ya raba Naira dubu goma-goma ga sama da mutane dubu daya da ri biyar. Idan an juya ga ‘yan jam’iyya kuma, Sanatan ya raba motoci ga shugabannin kananan hukumomin yankin tare da raba wa sakatarorinsu mashina. Haka su ma shugabannin jam’iyya ba a bar su a a baya ba, domin Sanatan ya ba wa kowane shugaban jam’iyya da sakatarensa babur a kananan hukumomi 13 da ke yankin.

A nasa jawabin Sakataren kungiyar, Kwamared Sagiru Ibrahim Gadanya ya yi kira ga matasan da su kula da tsirarun mutanen da ba sa son ci gaban yankin Arewacin Kano, wato ‘yan jam’iyyar PDP da kuma tsagin APC Kwankwasiyya bisa rubuce-rubucen karya da suke yi akan Sanata Barau domin burinsu shi ne su kawo fitina da nakasu a ci gaban matasan yankin.