Hukumar Tsaro ta NSCDC reshen Jihar Kwara ta kama mutane hudu a Karamar Hukumar Irepodun bisa zargin yi wa wata mata fyade sannan suka kashe ta.
Rahotanni sun ce an tsinci gasar matar mai suna A’isha Sani a cikin daji bayan da jami’an tsaro suka bazama neman ta.
- Rana ba ta karya: Ranar sake bude sufurin kasa da kasa a filin jirgin saman Kano ta zo
- Maniyyatan da aka yi wa rigakafin COVID-19 ne kadai za a bari su shiga Saudiyya
Wadanda ake zargin, a cewar kakakin NSCDC a jihar ta Kwara, Babawale Zaid Afolabi matasa ne masu shekaru 15 zuwa 19.
Ya ce sakataren Kungiyar Fulani na Esie/Ijan, Alhaji Musa Waziri ne ya kai rahoton zuwa ofishin hukumar.
Babawale ya kara da cewa an tsinci gawar A’isha tsirara ne da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar 4ga watan Fabrairun 2021 da raunuka a sassan jikinta da dama.
“Mun kama uku daga cikin wadanda ake zargi kuma a bayanansu sun nuna cewa sun kama wata mata ’yar Fulani ce bisa zargin satar kashu amma daga baya ta tsere.
“Bincikenmu ya gano cewa babban wanda ake zargi ya aika sauran masu aika-aikar su uku su kamo masa daya matar saboda ya yi amfani da ita.
“A kokarinsu na yi mata fyaden, ta sami nasarar ji masa rauni a kafadarsa ta dama da kuma wuyansa,” inji shi.
Ya ce tuni aka tisa keyar wadanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka domin fadada bincike.