Rundunar jami’an kare al’umma ta Civil Defence ta jihar Kwara ta tabbatar da cewa an harbe mutum uku a garin Lafiagi da ke karamar hukumar Edu a ranar Juma’ar da ta gabata.
Mai Magana da Yawun Rundunar, Mista Kunle Bilesanmi ya fada wa manema labarai cewa wadansu mutane sun kone wani sashe na gidan Sanata Mohammed Sha’aba na APC daga jihar Kwara.
Bilesanmi ya bayyana cewa rundunar ba ta tantance wadanda aka harbe ba.