✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matasa sun yi zanga-zanga a Fadar Sarkin Musulmi

Matasan sun ce dole a hukunta wani matashi da suka zarga da batanci ga Annabi

Wasu matasa da suka yi dandazo da yammacin ranar Alhamis a Fadar Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, sun ce suna gudanar da zanga-zanga ne don neman a hukunta wani matashi da aka zarga da yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Matasan dauke da alluna sun zagaye Fadar Sarkin Musulmi suna cewa dole sai an dauki mataki a kan wannan matashi, ba za su lamunce ba.

  1. An gano wani sabon nau’in COVID-19 a Najeriya
  2. EFCC na neman hadimin Tambuwal kan damfarar N2.2m

Ana zargin matashin ne mai suna Isma’ila Sani Isah Gobirawa da wallafa kalaman batanci a shafinsa na Facebook ranar Laraba, yana nuna bacin ransa saboda ya nemi aiki a karamar hukuma bai samu ba.

Ahmad Dikundikun, daya daga cikin wadanda suka yi magana a madadin matasan, ya ce, “Mun san gidan su yaron da [mahaifinsa] amma dai muka zo Fadar Sarkin Musulmi domin a dauki matakin da shari’a ta amince da shi…”

Shi ma Zannan Goronyo cewa ya yi dole a hukunta wanda ake zargi domin su ba su yarda da cewa wanda suke zargin ba shi da hankali ba.

A cewarsa, “Ta yaya wanda ba shi da hankali ke yin Facebook, ya sayi data, ya san ya goge rubutu bayan ya yi?”

‘’Yan sanda na bincike’

Jagoran ’yan sandan da suka hana matasan shiga Fadar Sarkin Musulmi, M.Y. Maru, ya shaida musu cewa wanda ya yi kalaman yana hannun jami’an tsaro wadanda suke gudanar da bincike a kan laifin da ake zargin ya aikata.

Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda Ibrahim Abdullahi, lokacin da yake magana da jagororin matasan a Hedkwatar Rundunar da ke Sakkwato, ya tabbatar musu cewa za a gabatar da wanda ake zargin a gaban kotu ranar Litinin mai zuwa.

Ya kuma roke su da kada su dauki doka a hannunsu.

Wadanda suka karanta abin da ake zargin matashin ya rubuta sun ce ya kuma yi batanci tare da cin zarafin wani mutum a unguwarsu wanda ya ce ya hana shi takardar kama aiki duk da yana da matsalar kudi.

Mutane da dama dai sun yi tir da abin da matashin ya aikata.