Wasu matasa a yankin Anaku da ke Karamar Hukumar Ayamelum ta Jihar Anambra, sun yi garkuwa da daya daga cikin sojojin da aka tura don wanzar da zaman lafiya a yankin mai fama da rikici.
Bayanai sun ce matasan sun yi awon gaba da sojan tare da bindigarsa.
- Mawakiya Rihanna ta sake samun juna-biyu da Rocky
- Na yanke kauna daga mutanen da ke zagaye da Buhari —El-Rufai
An tura jami’an tsaro da suka hada da sojoji domin dawo da zaman lafiya a yankin a yayin da aka ce matasan karkashin jagorancin shugabansu wanda aka fi sani da ‘Vulture’ sun kashe mutum takwas tare da raunata da dama a yankin Omor a ranar Litinin da ta gabata.
A halin da ake ciki, Gwamna Charles Soludo, ya umarci matasan yankin da su gaggauta sakin sojan tare da mayar masa da bindigarsa.
Shugaban kwamitin mika mulki na Karamar Hukumar Ayamelum, Cif Livinus Onyenwe ne ya bayyana umarnin gwamnan.
A cewarsa, gwamnan ya kuma umurci jami’an tsaro da su yi duk abin da Kundin Tsarin Mulki ya tanadar don ganin sun ceto sojan, tare da dawo da bindigarsa.
Onyenwe, ya ce gwamnan ya bayar da umarnin cewa jami’an tsaro za su ci gaba da kasancewa a garin har sai an gano wadanda suka aikata laifin.
A cewarsa, a kokarin mayar da martani, sojojin sun ruguza gidan shugaban kungiyar matasan, da kuma wasu matasa da ake zargin suna cikin kungiyar da ta kashe mutane a yankin.
Jihar Anambra dai kamar wasu jihohin Najeriya na fama da hare-haren ‘yan bindiga, wanda da dama ake kyautata zaton ‘yan awaren Biyafara ne ke daukar nauyin kai hare-haren.