✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun tubure kan tsige Shugaban Majalisar Dokokin Filato

Fusatattun matasan sun hallara a Majalisar tun da misalin karfe 4.00 na Asubahi.

Gomman matasa sun tubure inda suka mamaye Majalisar Dokokin Jihar Filato domin nuna adawa da tsige shugabanta, Honarabul Abok Ayuba Nuhu da aka yi a ranar Alhamis.

Aminiya ta ruwaito cewa, fusatattun matasan sun hallara ne a Majalisar tun da misalin karfe 4.00 na Asubanci inda suka fara gudanar da zanga-zangar tumbuke Honarabul Nuhu da aka yi a makon jiya.

Bayanai sun ce bayan tsige Honarabul Nuhu, an kuma maye gurbinsa da Sanda Yakubu, wanda ya fito daga mazabar Pingana ta Karamar Hukumar Bassa da ke Jihar.

Mambobi 16 daga cikin 24 na majalisar ne suka kada kuri’ar amincewa da tsige shi a zaman majalisar na ranar Alhamis wanda Mataimakin Shugaban Majalisar, Saleh Yipmong ya jagoranta

An ruwaito cewa akwai rashin jituwa tsakanin Gwamna Simon Lalong da Honarabul Nuhu tun bayan harin da aka kai a unguwar Yelwan Zagam da ke yankin Jos ta Arewa, inda aka kashe mutane da dama.

Bayan harin ne Shugaban Majalisar ya fara sukar gwamnan a fili sannan ya kuma daina halartar ayyukan gwamnati a jihar.