Majalisar Matasan Najeriya (NYCN) ta bukaci Shugaba Buhari da kada ya bari a yi zagon kasa a kokarinsa na bude asusun tallafa wa masata (NYIF) ta hanyar siyasantar da hukumar.
Matasan sun ce kiran ya shafi “sauran shirye-shiryen da suka hada da na bude cibiyoyin fasahar sadarwar zamani a fadin Najeriya”.
NYCN ta ce matsalar tsaro da kashe-kashe na dagula wa Gwamnatin Buhari lissafi wajen kawo sauye-sauye masu ma’ana.
Don haka ta nemi ya kara jajircewa ya magance matsalar Boko Haram da garkuwa da mutane da ‘yan fashin daji da sauran masalolin tsaro.
A wasikarsu ga Shugaban Kasar, shugaban kungiyar Solmon Adodo ya bayyana goyon baya da shirye-shiryen gwamnati na kawo cigaba kasa.
Adodo, a wasikar da ya karanta a gangamin wayar da kai game kafofin tattalin arziki a Abuja, bayan Ranar Matasa ta 2020 ya danganta matsalolin tsaro a Najeriya da manyan sauye-sauyen da kasar ke fuskanta.