Wasu fusatattun matasa sun kori sarkin garinsu daga fadarsa sakamakon zargin sa da kin yin abin da ya dace a matsayinsa na sarki mai martaba.
Fusatattun matasan sun fatattaki Mai Martaba Odaji Ipuole daga Masarautar Okuku da ke Ogbaniko a Karamar Hukumar Yala ta Jihar Kuros Riba ne a yammacin ranar Laraba.
Matasan sun zargi sarkin da kin kiran taro na bai-daya domin magance matsalolin da suka dabaibaye jama’arsa.
Sun bayyana cewa wannan hali nasa na ko-in-kula yana tada zaune tsaye a yankin.
- ’Yan fashi sun duro daga bene ana tsakar tuhumar su a kotu
- Masu kamun kifi da ISWAP ta kashe a Borno sun karu zuwa 31
- Rikicin Sarauta: Alkalan Kano za su gurfana a Abuja kan umarni masu karo da juna
Matasan sun ce za a ci gaba da rufe fadar har sai lokacin da sarkin ya bayar da tabbacin zai gyara halinsa, ya kuma yi alkawarin zai rika daukar mataki a kan abin da ya dace a yankin.
Pius Ireti daya daga cikin matasan da suka kori sarkin ya ce kafin su dauki matakin, sun sha bai wa sarkin shawarwari amma ya ki ji.
Jami’ar hulda da jama’a na ’yan sandan jihar Kuros Ribas, Irene Ugbo, ta ce suna gudanar da bincike kan lamarin.