Wasu fusatattun matasa sun kashe tare da kone gawarwakin wasu mutum biyu da ake zargi da garkuwa da mutane kurmus a jihar Filato.
Lamarin ya faru ne a gundumar Anpam da ke Karamar Hukumar Mangu ta jihar.
- Gyaran Tsarin Mulki: Yadda Aisha Buhari ta ‘kasa’ fitar wa mata kitse a wuta
- NAJERIYA A YAU: Sirrin Da Bello Turji Ya Bayyana Mana A Maboyarsa
Wakikinmu ya ce matasan sun kuma banka wa gidaje akalla 13, mallakin makiyaya, wuta a yankin bayan kone mutanen.
Sai dai Aminiya ta gano cewa lamarin ya jefa zama dar-dar a zukatan mazauna yankin.
Mai magana da yawun ’yan sanda a jihar, ASP Ubah Gabriel, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakikinmu.
Ya ce, “Tabbas lamarin ya faru, kuma an kone mutanen da ake zargin masu garkuwa da mutane don karbar kudin fansa ne a Mangu. Muna sane da faruwar hakan.
“Tuni Kwamishinan ’Yan Sanda ya ba da umarnin aikewa da dakaru yankin don su kwantar da kura. Yanzu haka ana can ana tattaunawar masu ruwa da tsaki a yankin don gano musabbabin harin da kuma kiyaye yiwuwar ramuwar gayya,” inji kakakin.