✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun kona coci saboda mutuwar matashi a Kaduna

A kwanakin baya ne wadansu matasa suka kona wani coci saboda rasuwar wani matashi a Unguwar Bayan Dutse da ke  Narayi a Kaduna Jihar Kaduna.…

A kwanakin baya ne wadansu matasa suka kona wani coci saboda rasuwar wani matashi a Unguwar Bayan Dutse da ke  Narayi a Kaduna Jihar Kaduna.

Matashin mai suna Sylebester Friday, dan shekara 21 yana aiki ne a cocin mai suna Celetial a unguwar. Bayanan da suka fito daga yankin sun nuna cewa matasan sun dauki matakin kona cocin ne saboda suna zargin wani faston cocin mai shekara 78, mai suna Babatunde Shitu da hannu wajen mutuwar matashin.

Shi dai marigayi Sylebester, an tsinci gawarsa ce a bayan cocin, inda yake aiki, wanda hakan ya sa wadansu matasan suke zargin kamar an yi tsafi da shi ne. Hakan ya sa suka kai wa faston hari da nufin hallaka shi, yayin da shi kuma ya nemi mafaka a wani ofishin ’yan sanda da ke unguwar.

Aminiya ta gano cewa kariyar da ’yan sanda suka bai wa faston ce ta harzuka matasan, inda suka bukaci a ba su shi amma ’yan sanda suka ki. kin ba da shi ne ya sa suka kona cocin sannan suka kuma far wa ofishin ’yan sandan, inda suka kona wani sashe nasa.

Narayi unguwa ce da akasarin mazaunanta Kiristoci ne amma duk da haka hatsaniyar sai da ta janyo guje-guje a yankin, inda mutane suka rika gudu domin kauce wa abin da ka iya biyowa baya.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Aliyu Muktar ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce randunar ta yi nasarar kama wadansu daga cikin matasan. Ya tabbatar da cewa faston yana hannunsu, a yayin da suke ci gaba da binciken lamarin. A cewarsa, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar ya bai wa jami’ansa umurnin kamawa tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin lamarin.

Gwamnan Jihar, Malam Nasiru El-Rufa’i bai bata lokaci ba wajen fitar da sanarwa  dauke da sa hannun kakakinsa Samuel Aruwan, inda ya yi Allah wadai da kona cocin. Ya kuma ba da umarnin yin bincike domin sanin musabbabin rasuwar matashin. Ya nemi jama’a su kauce wa daukar doka a hannunsu; domin a cewarsa gwamnati ba za ta yarda wadansu tsirari su daukar hukunci a hannunsu ba.