✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun kashe dan banga a kasuwa a Neja

Rikici ya kaure tsakanin ’yan bangar da wasu fusatattun matasa a Kasuwar Bosso.

Wani dan banga a Karamar Hukumar Bosso a Jihar Neja ya rasa ransa a  sakamakon arangama da suka yi da wasu matasa a Minna, hedikwatar jihar.

Rahotanni sun nuna cewar lamarin ya faru ne a lokacin da ’yan banga suke kokarin tilasta wa ’yan kasuwa tashi daga Kasuwar Bosso zuwa sabon matsuguni da aka gina musu.

Wata majiya ta ce dan bangar ya rasa ransa ne sakamakon buga masa dutse da wasu matasa suka yi a kai.

Wani wanda lamarin ya faru a kan idonsa ya ce matasan sun fusata ne lokacin da ’yan bangar suka fara kwace kayayyakin ’yan kasuwar da suka ki komawa sabuwar kasuwar da aka ware musu.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin ’Yan Sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, amma hakarsa ba ta cim ma ruwa ba.