Gamayyar Matasa masu Kare Dimokuradiyyar da Shuganci nagari ta yi tir da karin farashin man fetur da na wutar lantarki wanda ta ce ya kara kawo tsadar rayuwa a Najeriya.
Shugabannin kungiyar sun koka cewa tun da gwamnati mai ci ta hau a shekar 2015 ‘yan Najeriya ke ta fama da karin farashin muhimman abubuwa.
“Yadda Gwamantin ke yin yadda ta ga dama ya kawo tashin farashin mai daga N87 zuwa N162; lantarki daga N22 zuwa N66; harajin kayan da aka saya ya zama 7.5% daga 5%; Dala ta koma N480 daga N195; bashin kasashen waje ya karu daga Dala biliyan 9 zuwa biliyan 27.
“A karkashin gwamnatin nan manyan laifuka sun karu, ta’addanci da fashin daji da garkuwa da mutane da fashi da makami da kuma cin zarafin mata, fasakwauri, talauci, yunwa da fatara da masu gudun hijira da rashin aikin yi da masu daina zuwa makaranta duk sun karu, kuma hakan bai dace ba.
Kungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta dauki matsalolin ‘yan Najeriya da muhimmanci ta kuma magance su domin samun cigaban kasa.
“Do haka muke kiran ‘yan Najeriya da su sanya bakaken kaya domin nuna bacin rai kan wahalar da suke ciki, kafin daukar wani mataki da zai kyautata rayuwar Najeriya da ‘yan Najeriya”, inji sanarwar da shugaban kungiyar Haruna Yusuf Abba da sauran jami’ai suka fitar.
Tuni dai Gwamnatin Tarayya ta bakin hukumar kula wutar lantarki (NERC) ta yi bayani cewa karin farashin wutar lantarki ba zai shafi talakawa ba.
A bayanin da NERC da kamfanonin rarraba wutar, sun ce karin ya kebanci masu samun ta na akalla awa 12 ne a kullum, amma banda talakawa da wadanda wutarsu ba ta kai kilowatt 50 ba.
Tuni dai gwamnatin ta ce tana daukar matakai domin ganin farashin kayan abinci da yake hauhawa ya ragu.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamatinsa na tattaunawa da kungiyoyin masu kayan abinci domin ganin yadda za a magance yadda ‘yan kasuwa ke tsawwala farashi.
Buhari, a jajensa ga wadanda suka yi asara a ambaliyar da aka samu a jihohi ya ba da izinin shigo da wasu kayan abinci domin yi wa tufkar hanci.
Game da karin farashin man fetur, masana sun ce abu ne da babu makawa a kansa, saboda yadda kasuwar danyen mai ta juya a fadin duniya.
Gwamntin ta kuma kafa rundunonin tsaro daban-daban domin tabbatar da zaman lafiya, wanda ko a ranar Asabar, sai da suka sanar da kama ‘yan bindiga 100 tare da kwato makamai da dubban dabbobi tare da tarwatsa sansanonin bata-gari a yankin Arewa maso Yamma.