✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matasa na zanga-zanga a Gashuwa bayan soja ya bindige direba

Sai dai Gwamnan Jihar ya bukaci a kwantar da hankula.

Wasu fusatattun matasa sun fantsama titunan garin Gashuwa, hedkwatar Karamar Hukumar Bade ta Jihar Yobe suna zanga-zanga kan kisan wani direban babbar mota da ake zargin wani soja aikatawa.

Matasan dai sun rika kona tayoyi yayin da suka tunkari ofishin ’yan sanda na garin.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa an bindige direban, mai suna Mohammed Gashuwa, ne lokacin da yake kokarin kaucewa wani gidan mai, a daidai lokacin da ya hangi motar sojoji da wasu kuma a kan babura.

Ya ce masu ababen hawan sun tsorata da yanayin sojojin, inda suka yi kokarin guduwa, amma sojojin suka yi gargadin cewa za su harbi duk wanda ya gudu.

To sai da ya ce firgitar da direban babbar motar ya yi ta sa ya fara gudu, inda daya daga cikin sojojin ya bindige shi nan take.

Wani daga cikin iyalan mamacin ya ce tuni aka riga aka yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, Baturen ’Yan Sanda (DPO) na yankin Bade bai amsa kiran wakilinmu ba don jin ta bakinsa a kan lamarin.

To sa dai Gwamnan Jihar ta Yobe, Mai Mala Buni, ya yi kira da a kwantar da hankali.

Gwamnan, a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Mamman Mohammed ya fitar ranar Asabar, ya ce tuni ya bayar da umarnin a gudanar da zuzzurfan bincike don a dauki matakin da ya dace a kai.