✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa 3 sun shiga hannu kan aikata fashi a Gombe

Waɗanda ake zargin sun amsa aikata laifin sa ake zargin su da shi.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wasu matasa uku kan zargin aikata fashi da makami a wani gida da ke unguwar Tudun Wada a jihar.

Kakakin rundunar, ASP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

A cewarsa, a ranar 2 ga watan Oktoba, 2024, rundunar ta samu ƙorafi daga wani mutum mai suna Alhaji Isah Suleiman dangane da fashin da aka yi masa.

Sanarwar ta bayyana cewa wasu matasa ne dauke da makamai suka kai hari gidan mutumin da ke unguwar Tudun Wada, Pantami.

Barayin sun ɓalla gidan ne suka shiga, inda suka kai wa mutumin hari, sannan suka yin awon gaba da kayayyaki masu yawa.

Kayayyakin da suka sace sun hada da babur kirar Haojue UD, wayoyin salula guda shida da fanka guda daya da bandir na zannuwa da kayan ado da kuma dutsen guga na lantarki.

Matasan da aka kama su uku suna hannu, amma na huɗun ya tsere lokacin da ‘yan sanda suka kai samame.

Kakakin  ya ce a yayin bincike, waxanda ake zargin sun amsa aikata laifin.

Bincike ya nuna cewar sun ƙware wajen aikata ire-iren waxannan laifuka a jihar.