✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa 2500 ke cin gajiyar shirin N-Power a Jihar Gombe – Maryam Mele

Mai bai wa Gwamnan Jihar Gombe Shawara kuma Mataimakiya ta Musamman a Ofishin Mataimakin Shugaban kasa kan Walwalar Jama’a, kuma Shugabar Shirin samar wa matasa…

Mai bai wa Gwamnan Jihar Gombe Shawara kuma Mataimakiya ta Musamman a Ofishin Mataimakin Shugaban kasa kan Walwalar Jama’a, kuma Shugabar Shirin samar wa matasa aiki na N-Power, Hajiya Maryam Isa Mele, ta ce matasa 2500 ne suka cika fom din N-Power kuma suke karbar alawus din Naira dubu 30 duk wata daga cikin matasa dubu 200 da ake son samarwa aiki a Najeriya.

Hajiya Maryam Isa Mele, ta bayyana haka ne lokacin da take zantawa da Aminiya a ofishinta don mayar da martani kan koke-koken da matasan da suka cika fom din shirin N-Power suke yi cewa an dauki wadansu amma an yi watanni ba su samu alawus ba.

Ta ce ba daga ofishinta ake biyan su ba, kuma matsalar tasu ce domin lokacin cika fom din an gargade su cewa su kula sosai su tabbata sun sa lambar BbN dinsu don da ita za a yi amfani wajen biyansu. Ta ce ofishin yana kula da mutum dubu 200 ne don haka a kan mutum daya ba za a saurari mutum daya ba, sai an gama da wadansu aiki ya ragu kafin a fara neman yadda za a gyara na wadanda suke da korafi.

 Shugabar ta ce lokacin da aka fara shirin, kimanin mutum 700 ne suka yi kuskuren cika fom dinsu, kuma ta ce ita take sa wa a gyara musu da kwamfutarta kyauta a ofishinta, amma duk da haka wadansu ba sa godiya sai bakaken maganganu.

“Gyare-gyaren da muka rika yi musu yanzu kusan an gama bai wuce mutum 50 cikin 700 ba, su din ma za a gyara musu ba za mu biye musu ba,” inji ta.

Ta ce dalilin da ya sa tun farko suke ta yi wa matasan gargadin cewa su bi a hankali wajen cike fom din ke nan don gudun samun matsala, domin idan lambar BbN din mutum ba ta yi daidai da sunan asusun bankinsa ba, ba zai samu kudinsa ba.

Hajiya Maryam Mele, ta ce matasa 2500 ne suka cika fom din N-Power suke karbar alawus din Naira dubu 30 duk wata daga cikin matasa dubu 200 da ake son samarwa aiki a Najeriya, kuma a duk wata Naira miliyan 86 ne yake shigowa Gombe  da sunan alawus din N-Power, “Ka ga ashe gwamnati tana kokari wajen rage zaman kashe wando sai dai yanzu haka wadansu ba sa zuwa aikin,” inji ta.

Ta gode wa Gwamnatin Jihar Gombe kan yadda take taimaka musu da kayayyakin aiki da motocin gudanar da aikin sannan ga ofishin da ta ba su inda suke gudanar da ayyukansu, domin a baya ba su da ofishi kame-kame suke yi.