Wasu matasa biyu – dan shekara 17 da dan shekara 27 – sun mutu a cikin wani masai da ke yankin Sabon Gari a Karamar Hukumar Fagge ta Jihar Kano.
Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, ne ya bayyana hakan a Kano a ranar Lahadi, inda ya ce matasan sun mutu yayin da suke kokarin yashe masan.
- Diphtheria: Cutar sarkewar numfashi ta bulla kananan hukumomi 13 a Kano
- An kama mutum 18 da ake zargi da aikata fyade a Borno
Ya bayyana cewa daya daga cikin matasan mai shekara 27 a duniya, yana tsaka da aiki a cikin masan sai ya makale, wanda daya abokin aikin nasa ya yi kokarin ceto shi, amma shi ma ya makale.
“Mun samu kiran gaggawa game da lamarin kuma nan da nan muka aike da tawagarmu zuwa wurin,” in ji shi.
Ya kara da cewa Hukumar Kashe Gobara ta ciro matasan biyu a sume, inda suka kai su Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad wanda daga bisani likita ya tabbatar da rasuwarsu.
Abdullahi ya kuma bayyana cewa an mika gawar matasan ofishin ‘yan sanda na Sabon Gari don gudanar da bincike.
Ya danganta mutuwar matasan da yawan zafi da ke cikin rami tare da rashin samun isasshiyar iska.