✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar Tinubu ta ba wadanda ambaliyar TradeMore ta shafa a Abuja N250,000

Kowanne daga cikin giadajen da ambaliyar ta shafa ya samu dubu 250

Matar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a rukunin gidaje na TradeMore da ke Abuja da Naira dubu 250 kowannensu.

A ranar 23 ga watan Yunin da ya gabata ce dai wata mummunar ambaliyar ruwa ta shafe kusan ilahirin gidajen da ke rukunin gidajen wadanda ke unguwar Lugbe a Abuja.

Da take jawabi a karkashin shirinta mai suna Renewed Hope Initiative, Remi, wacce matar Mataimakin Shugaban Kasa, Nana Shettima ta wakilta, ta bayyana alhininta ga mutanen.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Busola Kukoyi, ya fitar ranar Alhamis, Remi ta ce kodayake babu tabbacin ambaliyar ba za ta sake faruwa tun da har yanzu ana cikin damuna, amma tana fatan taimakon zai rage musu radadin da suke ciki.

Ta ce duk da cewa har yanzu tana kan aikin yi wa shirin nata rajista da gwamnati, amma ba zai yiwu ta zuba wa mutanen ido haka kawai ba.

Da yake jawabi a madadin sauran mazauna rukunin gidajen, shugaban kungiyarsu, Dokta Adewale Adenaike, ya gode mata kan tallafin musamman a lokacin da suke cikin tsananin bukata.

Kowanne daga cikin gidajen da ambaliyar ta shafa dai ya rabauta da tallafin Naira dubu 250, kuma jimillar gidaje 57 ne suka amfana da shi.