✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana fargabar ruwa da iska sun kashe mutum 2,000 a Libya

Gwamnatin Gabashin Libya, ta yi ikirarin cewa sama da mutum 2,000 sun rasu, wasu dubban kuma sun bace

Ana fargabar mutum kimanin 2,000 sun mutu a kasar Libya sakamakon ruwa da mahaukaciyar idakr Daniel da ta kaɗo daga Tekun Mediterranean.

Ruwa da iskar sun shanye gidaje, suka rusa wasu tare da haddasa zaftarewar kaka, ta yi barna a kasashen Turkiyya, Bulgaria da  Greece — inda ta faro.
Fira Ministan gwamnatin Gabashin Libya, Oussama Hamad,  ya yi ikirarin “ya ce sama da mutum 2,000 sun rasu, wasu dubban kuma sun bace” a birnin Derna kadai, amma dai jami’an lafiya ko halastacciyar gwamnatin kasar ba su tabbatar da alkaluman da ya bayar ba.

Duk da cewa alkaluman da kafofin yada labarai da ke Gabashin Libya suke bayarwa ke nan, amma wasu bayanan sun nuna girman barnar bai kai haka ba.

Da farko dai Mohamed Massoud, mai magana da yawun gwambatin Hamad da ke Benghazi, ya ce “aƙalla mutane 150 ne suka rasu sa sakamakon ruwa da mahaukaciyar guguwar Daniel a yankin Derna, da ke Lardin Jabal al-Akhdar.

“Iftila’in ya haddasa mummunar asara ga dukiyoyin al’umma da kayan gwamnati,” kamar yadda ya bayyana wa AFP.

Ana fargabar akwai daruruwan mutane da suka makale a wurare masu wuyan zuwa a sakamakon ambaliyar, a yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Hukumomin yankin Gabashin Libya sun ce sun daina jin ɗuriyar wasu sojojinsu tara a yayin da suke tsaka da gudanar da aikin ceton.

Hamad da kansa yake jagoranta aikin ceto inda ya jagoranci sauran ministoci zuwa yankin da abin ya faru domin gane wa idonsu.

Kwararru sun bayyana guguwar Daniel a matsayin mai matukar hatsari bayan da ta hallaka mutum 27 a kasashen Turkiyya, Bulgaria da Greece a yan kwanakin nan.