Mutane da dama sun makale a gidajensu bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya haddasa ambaliya a Karamar Hukumar Alimosho da ke Legas.
Ruwan saman na sama da sa’o’i shida an fara shi ne da misalin karfe 6 na safe, kuma ambaliyar ta shanye yawancin tituna da gadoji da ke birnin.
Hakan ya tsaiko ga zirga-zirgar ababen hawa, a yayin da motocin haya ke guje wa wuraren da abin ya shafa.
Unguwannin da abin ya fi shafa sun hada da Abule-Egba, Command, Agege da unguwar Egbeda.
- Yunwa: Jama’a sun daka wa motar Dangote wawa a Katsina
- Hisbah ta cafke ’yan kasar waje kan aikata badala a Kano
Masu aikin ceto daga hukumomin jihar da na gwamnatin tarayya suna ci gaba da aiki domin ceto wadanda suka makale.
Ko’odinetan Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a shiyyar Kudu maso Yamma, Ibrahim Farinloye, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A wani sako da ya aike ta WhatsApp, ya shawarci mazauna yankin Command da su bi wasu hanyoyin daban, idan za su fita, saboda ambaliyar ta mamaye gadar.