An tara ‘yan kallo a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano lokacin da matar Shugaban hukumar tsaro ta DSS, Aisha Magaji Bichi, ta hana dan takarar Gwamna na jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, shiga jirgi.
Aminiya ta gano rikicin ya fara ne bayan da tawagar dan takarar ta haifar wa tawagar Aisha tsaiko da kuma jinkirin isa masaukin manyan baki na filin jirgin.
- Ni na dora Bala a Gwamna, kuma ni zan sauke shi – Tsohon Wazirin Bauchi
- Hajji 2023: An ba wa jihohi kujerun maniyyata 75,000
An ce hakan ya sa jami’an tsaron da ke tare da ita suka sauko daga mota domin buda wa uwargijiyarsu hanya.
Lamarin da ya haifar da hatsaniya a tsakanin jami’an tsron da hadiman dan takarar.
“Al’amari ya yi kamari ne bayan da Aisha ta fada wa Abba ba za su shiga jirgi daya ba kamar yadda aka tsara da farko.
“A nan ta hango daya daga cikin hadiman Abba, Garba Kilo na daukar bidiyonta (da waya),” in ji wata majiya.
Bayanai sun ce an garzaya da Kilo Asibitin Koyarwa na Aminu bayan da ya ci duka bisa umarnin Aisha.
Majiyar ta ce, “Sun yi masa [Kilo] dukan fitar hankali, wanda hakan ya sa Abba cewa atafau jirgi daya za su shiga kamar yadda aka tsara, inda hakan ya kara tinzara ta har da ya kai ga ta ba da umarnin a tsare shi.”
Cikin haka ne aka ce wata tawagar ‘yan sandan sirri ta kange dan takarar Gwamnan har jirgin da Aisha ta shiga ya tashi.
Wani babban jami’in DSS da ya bukaci a sakaya sunansa wanda kuma a gabansa komai ya gudana, ya ce lamarin abu ne da za a iya hana aukuwarsa.
Ya kara da cewa ba daidai ba ne bayyana mai dakin Shugaban DSS din da mafadaciya.
Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun dan takarar, Sanusi Bature, ya ci tura.
Shi kuwa Kakakin DSS, Peter Afunanya ya ce, “Babu wanda jami’an suka daka, mukan sa a bi doka kamar yadda tsari ya tanadar.
“Batun cewa an tsare dan takarar ba shi da tushe balle ya ja hankalin hukumar ko ma duk wata kafar yada labaran da ta san ya kamata.