✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matar Sheikh Abubakar Gumi ta rasu

Za a yi jana'izarta bayan Sallar La'asar a gidan Sheikh Gumi da ke Kaduna.

Allah Ya yi wa matar fitaccen malamin addinin Islama, marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Hajiya Aminatu Bintu, rasuwa.

Sheikh Abubakar Mahmud Gumi shi ne mahaifin Sheikh Dokta Ahmad Abubakar Gumi da dan uwansa, Janar Abdulkadir Gumi.

Marigayiya Hajiya Aminatu Bintu, ita ce mahaifiyar Birgediya Janar Abdulkadir Gumi, kuma ta rasu ne a ranar Asabar da safe a Babban Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna, tana da shekara 88.

Za a sallace ta da bayan Sallar La’asar a Masallacin marigayi Sheikh Abubakar Mahmdu Gumi, inda yanzu Dokta Ahmad Gumi yake da zama a Kaduna, idan Allah Ya kai mu.