Abu mai wuya ne a ce mutum ya dade a cikin ruwa, in dai ba don sha’awa ko ninkaya don rage zafi ko kuma wanke daudar jiki ba.
Kuma komai dadewar mutum a cikin ruwa ba zai wuce ’yan sa’o’i ba, duk nacinsa sai ya fito, in ya so daga baya ya koma idan yana bukatar haka.
Sai dai abin ba haka yake ga wata mata ’yar kasar Indiya ba.
Matar mai suna Pataruni Gosh da ke zaune a yammacin Bengal ta kasar Indiya, rayuwarta kacokam a cikin ruwa take yi, in kuwa babu ruwa kusa da ita to, ba za ta rayu ba.
Domin a kullum Pataruni a cikin ruwa take yini daga fitowar rana zuwa faduwarta.
Idan gari ya waye dattijuwar mai shekara 65 tun kafin rana ta fito sai ta nufi rafin kauyensu ta tsunduma ciki sanye da kayanta, ta yi zamanta a ciki kanta a waje, ba za ta fito ba sai rana ta fadi.
Haka Pataruni take yi a kullum tun tana da shekara 45 da haihuwa, ma’ana shekara 20 tana yini a cikin rafi babu fashi.
Kwana ne kawai ba ta yi a cikin ruwan, sai dai kullum idan ta shiga da sayin safiya sai rana ta fadi ta fito ta tafi gida ta kwanta, sai washe gari ta fito ta sake shiga rafin.
Likitoci sun ce matar tana fama da wata cutar fata ce tun 1998, wacce har yanzu ba a gano wace irin cuta ba ce, ga kuma fama da talauci wanda ya sa mata kaimin neman magani da samun waraka ya wuya ta a gare ta da kuma makusantanta.