✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar Aure: Rahama Sadau za ta saki sabon shirin mai dogon zango

Shirin na nan tafe nan ba ba da jimawa ba.

Rahama Sadau, fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, za ta fidda sabon shiri mai dogon zango mai taken ‘Matar Aure’.

Cikin wani sako da ta wallafa a shafukanta na dandalan sada zumunta, jarumar ta sanar da cewa shirin na nan tafe nan ba ba da jimawa ba.

Kamfaninta na Sadau Pictures ne zai gabatar da shirin kamar yadda ta bayyana.

Rahama ta kuma ce shirin zai haska wasu daga cikin fuskokin jaruman Kannywood kamar Aminu Shariff Momo, Yakubu Muhammed, Abdallahi Rikadawa, Fati Washa da sauransu.

Fostar fim din Matar Aure

Sai dai jarumar ba ta yi wani karin haske kan hakikanin alkibla ko abin da shirin zai kunsa ba.

Rahama ce da kanta ta marubuciyar wannan shiri mai taken Matar Aure, kuma ita ce mai shiryawa.

Yaseen Auwal da Afazazee Muhammed ne masu bayar da umarni.