Mata nawa daga daga Jihar Kano kuka sani shugaban kasa ya taba sauya sunayensu a jerin mutanen da yake son nadawa minista a tarihi?
A makon shekaranjiya ne Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sanar da sunan Maryam Shetty a cikin jerin sunayen wadanda yake so ya nada a matsayin minista.
- Juyin Mulki: Mali da Burkina Faso sun tura sojoji Nijar
- NAJERIYA A YAU: Yadda Zabin Ministocin Tinubu Ya Bar Baya Da Kura
Maryam fitacciyar ’yar soshiyal media ce, wadda ta dade tana gwagwarmaya a siyasar Najeriya; Sai dai sanar da sunanta ya bar baya da kura, inda mutanen suka yi wa Shugaba Tinubu ca, suna cewa lallai ba ta cancanta ba.
Ana cikin haka ne ya musanya sunanta da wata Dokta Mariya Bunkure a matsayin minista.
Aminiya ta ruwaito cewa da Maryam Shetty da Dokta Mariya ajinsu daya a firamare sannan sun yi jami’a daya.
Binciken Aminiya ya nuna cewa ba Maryam Shetty ba ce ta farko da aka sauya sunanta a Kano.
A shekarar 2014 Shugaban Kasa na wancan lokacin ya sauya sunan Jamila Salik daga Jihar Kano a matsayin minista inda ya maye gurbinta da Sanata Ibrahim Shekarau.
Da farko an tura sunan Jamila Salik ne, wadda a lokacin ta yi takarar majalisar jihar Kano a shekarar 2007.
Sai dai a lokacin ta rabu da Kwankwanso, sai Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da wasu mutanensa suka tura sunanta a Kano.
Sai dai daga baya an sauya sunan ta da Sanata Ibrahim Shekarau, wanda ya zama ministan Ilimi.