✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matan Kannywood sun fasa maka Sarkin Waka a kotu

MOPAN da haramta wa ’yan fim tsokaci kan dambarwar Ladin Chima a kafafen sada zumunta

Kungiyar Matan Kannywood ta Najeriya (K-WAN) ta janye karar da za su shigar da mawaki Naziru Ahmad Sarkin Waka a gaban kotu kan zargin bata wa mambobinta suna.

Sanarwar janyewar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na Kungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Najeriya (MOPPAN) na kasa, Al-amin Chiroma, ya fitar bayan wani taron gaggawa da aka gudanar a Kano.

Janyewar na zuwa ne bayan taron da MOPPAN ta shirya da hadin gwiwar dattawan Kannywood da kuma Kungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Arewa (AFMAN) kan dambarwar da ta biyo bayan ikirarin fitacciyar jarumar nan Ladin Chima, ta yi a hirarta da sashen Hausa na BBC.

Sanarwar da Al-amin Chiroma ya fitar bayan wani taron gaggawar ta ce dukkan bangarorin da abin ya shafa da masu ruwa da tsaki na Kannywood sun halarci zmaan kuma an cimma matsaya an shawo kan matsalar.

Ya kuma bayyana cewa taron ya haramta duk wani rubutu da ya shafi shafin Ladin Chima a shafukan sada zumunta.

Ya kara da cewa za a gudanar da wani taron kara wa juna sani na horar da ’yan Kannywood kan hanyoyin da suka dace na amfani da kafofin sadarwar zamani domin kauce wa faruwar irin haka a nan gaba.

Mahalarta taron sun hada da Auwalu Ismail Mashal, Mustapha Naburaska (Mashawarcin Gwamnan Kano a Kan Kannywood), Mohammad Ibrahim Gumel, Hadiza Muhammad, Abubakar Bashir Maishadda, Misbahu M. Ahmad, Naziru M. Ahmad, Alhaji Ibrahim Mandawari da sauransu.

Idan ba a manta ba a ranar Litinin kunngiyar K-WAN ta bai wa Naziru Sarkin Waka wa’adin kwana uku da ya nemi gafarar matan Kannywood ko kuma su maka shi a kotu.

Kungiyar ta neman mawakin ya yi haka ne saboda abin abin da ta kira bata sunan matan Kannywood a zargin da ya yi cewa wasu na ba da kansu domin a sanya su a fim.

A cewar kungiyar kalaman na Sarkin Waka ya zubar da kimar matan Kannywood.

Sarkin Waka ya yi zargin ne a wani bidiyo da ya fitar domin nuna takaicinsa kan yadda wasu ’yan Kannywood ke karyata Ladin Chima da ta ce ba a taba biyan ta abin da ya kai N50,000 a fim.

Daga baya dai kungiyar ta janye karar.