Masanin kiwon lafiya daga Jami’ar Ibadan, Dokta Yemi Raji, ya shawarci ’yan Najeriya da su rungumi matakan kariya a matsayin hanya mafi inganci wajen yaki da cutar koda.
Raji ya ba da shawarar hakan ne yayin zantawarsu da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Alhamis a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Shawarar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke bikin Ranar Koda ta Duniya ta 2023 wadda aka saba gudanarwa duk shekara a watan Maris.
Ya ce, cutar koda ta zama babbar matsala ga kasashen duniya, kuma Najeriya ma ba ta tsira ba.
Masanin ya lissafo wasu matakan da za a kiyaye domin kauce wa kamuwa da cutar koda, ciki har da:
- Kauce wa shan magani barkatai
- Daina amfani da magani ba tare da umarnin likita ko masanin kiwon lafiya ba
- Ziyartar asibiti duk lokacin da ake fama da wani rashin lafiya
- A rungumi dabi’ar shan ruwa da yawa, saboda hakan na taimaka wa aikin koda
- Takaita cin gishiri a abinci
- Yawaita ta’ammali da ’ya’yan itatuwa
- Guje wa yawan cin abincin gwangwani, da danginsa
Raji ya yi kira ga masu fama da cutar sukari da hawan jini da saura lalurorin da ka iya haifar da matsalar koda, da su ziyarci kwararrun wuraren da za su iya samun kulawar da ta dace.
(NAN)