✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matakan da mata za su bi don yin karbabbiyar Sallah (2)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili mai albarka. Muna fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon ma za mu ci gaba…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili mai albarka. Muna fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon ma za mu ci gaba da kawo muku cikakken bayani ne kan matakan da mata za su bi don yin karbabbiyar Sallah. Muna fata za ku bi bayanin sau da kafa don cin ribar darussansa. Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
A makon jiya mun tsaya ne a wurin da za ku yi sujuda, inda muka yi bayanin cewa a yayin sujuda a kan samu matsaloli, mun bayyana cewa, abin da ake so ku yi kafin lokacin sujuda shi ne, za ku fara da lankwasa gwiwowinku ne, sannan ku fara tafiya zuwa ga sujuda, daga nan ku dora tafin hannunku a kasa, sannan ku dora goshinku a kasa. A yayin sujuda ku tabbatar kan hancinku ya taba kasa. A lokacin sujuda ana so gabobin jiki su rika kallon alkibla, tun daga ’yantsun kafafu da na tafin hannu da sauransu. Daga nan ku karanta ‘Subhana Rabbiyal A’ala Wa bi Hamdihi, sau uku, ko biyar ko bakwai. Daga nan a dago daga sujuda.
Ga ci gaban bayanin:
A yayin dagowa daga sujuda, za ku yi kabbara, sannan a lokacin da kuke dagowar ana so ku fara da goshinku, sannan hancinku, sai hannuwanku. A lokacin da za ku zauna kafin komawa sujuda ta biyu, ana so duwawunku su zauna a kan dandamalin da kuke sallah, sannan yatsunku su kalli gefen dama, a lokaci guda ku dora tafin hannuwanku a kan cinyoyinku. Za ku zauna kadan, sannan ku sake yin kabbara, daga nan ku tafi zuwa sujuda ta biyu. Sannan ku sake yin addu’ar da kuka yi a lokacin da kuka yi sujuda ta farko.
Daga nan ku mike tsaye don kawo raka’a ta biyu, a lokacin da za ku mike tsaye, ana so ku fara da dago da goshinku, sai hancinku, sai hannuwanku, sai kuma gwiwonku, kafin ku kai ga mikewa tsaye gaba daya.
Bayan kun kawo raka’a ta biyu kamar yadda kuka yi ta farko, to za ku yi karatun tahiya. Abin da ake karantawa yayin tahiya:
“Attahiyatu lillahi, wassalawatu waddayibatu lillahi, assalamu alaika, ayyuhan-Nabiyyu wa rahamatullahi wa ala ibaadissalihineen. Asshadu an laa ilaha illallahu wa ash hadu anna Muahammadan abduhu wa Rasaluhu.”
A lokacin da kuke karatun tahiya, ana so ku dunkule yatsunku na dama, ku dora shi a kan cinyarku ta dama, sannan ku mikar da ’yar manuniyarku ta rika fuskantar alkibla, sannan idanunku su rika kallon dan yatsan naku. Za ku dora tafin hannunku na hagu a kan cinyarku ta hagu.
Idan tahiya ta biyu kuke yi, za ku iya karanta salatin annabi da sauran addu’o’i.
A lokacin da za ku yi sallama, za ku dago kanku daga kallon dan yatsanku, sannan  ku kalli bangaren dama kafin ku ce ‘Assalamu Alaikum Wa Rahamatullah, sannan ku sake kallon bangaren hagu kafin ku sake cewa “Assalamu alaikum wa Rahamatullah.”  
 karin bayani:
A lokacin da kuke karatun tahiya ta biyu na ambaci cewa za ku yi salatin annabi da kuma sauran addu’o’i, na tabbata wadansunku za su rika tambayar kamar wadanne addu’o’i ke nan. To addu’o’in sun hada da:
“Allahumma Inni A’azu bika Min Azabil kabri, wa min azabil Jahannam, wa min fitnatil mahya wal mamat, wa min sharril fitnatil masihid Dujjal”
“Allahumma inni Dhalamtu nafsee dhulman kaseeran, wa laa yagfiruth zunooba illa anta, fagfir lee maghfiratan min indika warhamnee innaka Antal ghafoorur Raheem.
Za ku yi karanta ire-iren wadannan addu’o’i a lokacin da kuke karatun tahiyar karshe.
A karshe ina fata wannan bayani zai gamsar da wadanda suke bukatarsa, Allah Ya taimake mu, amin.