Mataimakin Shugaban Jam’iar PDP mai mulki a Jihar Bauchi, Bala Hadith, ya ajiye mukaminsa.
Kazalika Masahawarcin Gwamnan a bangaren Kanann Hukumomi da Masarautu, Hassanu Yunusa Guyaba ya ajiye aikinsa a gwamnatin.
- An cafke masu yi wa ’yan fashi safarar makamai a Kaduna
- An kama mai gyaran wuta a cikin likitocin bogi masu aiki a asibitoci fiye da 100 a Kano
Takardar ajiye aikin da Guyaba ya aike wa gwamnan a ranar Laraba ta ce, “Na ajiye mukamina na Babban Mashawarcin Gwamna kan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu daga ranar Talata, 3 ga watan Janairu, 2023.
“Ina mika godiyata tare da iyalaina da abokan arziki da magoya baya ga Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya ga dacewar nada ni a wannan mukami — Muna godiya matuka,” in ji Guyaba.
A bangarensa, Mataikin Shugaban PDP Reshen Jihar Bauchi, Bala Hadith ya aike da takardar ajiye mukamin nasa ne ga Shugaban Jam’iyyar Hamza Akuyam.
Ya ce, “Ina sanar da kai game da wannan mataki da na dauka. Ina wa PDP fatan alheri.”
Kawo yanzu dai babu bayani game da dalilin ajiye aikin nasu.
Sai dai kuma hakan na zuwa ne a daidai lokacin da dambarwa ta kunno kai a jihar, kan tsige Wazirin Bauchi, Alhaji Muhammad Bello Kirfi, a ranar Talata, kan zargin rashin da’a ga gwamnan.
A ranar Laraba, ’yarsa, Honorabul Sa’adatu ta ajiye mukaminta na Kwamishinar Kungiyoyi, Kanana da Matsakaitan Sana’o’i ta jihar.