✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An shiga rudani kan ‘sauya shekar’ Mataimakin Gwamnan Sakkwato

Sanarwar da ya fitar ranar Alhamis ta ce babu kamshin gaskiya a labarin da ke cewa ya bar PDP

An shiga rudani bayan wasu sanarwar masu cin karo da juna kan ficewar Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Manir Dan’iya daga jam’iyyarsa ta PDP.

Da farko wata sanarwar ce ta fito ta nuna ya aike wa shugaban PDP na mazabarsa ta Kware cewa ya fice daga jam’iyyar, duk kuwa da cewa shi ne dan takararta na Sanata a Mazabar Sakkwato ta Arewa

Sai dai kuma daga baya aka ga wata sanarwar da ke karyata ta farko.

Sanarwar da ya fitar ranar Alhamis ta ce babu kamshin gaskiya a labarin da ke cewa ya bar PDP, ballanta a yi hasashen cewa zai koma APC.

“Na lura da wani labari da ke yawo cewa Mataimakin Gwamna Manir Dan’iya ya bar Jam’iyar PDP, to wannan labari karya ce tsagwaronta.

“Har yanzu Honorabul Manir Dan’iya halastaccen dan Jam’iyar PDP ne kuma mai goyon bayanta da kuma gwamnatin Sakkwato,” in ji wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan yada labaran mataimakin gwamnan, Aminu Abdullahi.