✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mataimakin gwamnan Ondo ya fice daga APC ya koma PDP

Mataimakin gwamnan Ondo, Agboola Ajayi ya fice daga jam’iya mai mulki ta APC ya koma babbar jam’iyyar adawa ta PDP. Agboola Ajayi ya bar APC…

Mataimakin gwamnan Ondo, Agboola Ajayi ya fice daga jam’iya mai mulki ta APC ya koma babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Agboola Ajayi ya bar APC ne a ranar Lahadi 21 ga watan Yuni a mazabar Apoi ta biyu da ke Karamar Hukumar Ose Edo a jihar Ondo.

Matakin Mataimakin Gwamnan na zuwa ne washegarin ranar da Kwamishina ‘Yan Sandan jihar, Bolaji Salami ya tare masa hanyar fita daga gidan gwamnati a garin Akure, babban birnin jihar.

Da yake cike takardar ficewarsa daga jam’iyar APC, mataimakin gwamnan ya ce dalilin ficewarsa daga jam’iyar ba sabon abu ba ne domin kowa na sane da halin da ake ciki.

Bayan ya cike takardar fitarsa daga jam’iyyar APC ne ya wuce zuwa ofishin jam’iyar PDP na mazabar ya kuma karbi katin zama dan PDP.

Rikicin Ajayi da kwamishinan ‘yan sanda

A ranar Asabar 20 ga watan Yuni kwamishinan ‘yan sandan jihar ya tare mataimakin gwamnan ya kuma hana shi fita da motarsa ta gidan gwamnati, lamarin da ake alakantawa da takun sakar da ke tsakaninsa da gwamnan jihar Rotimi Akeredolu.

A wani bidiyo mai tsawon sakan 41 da an ga lokacin da kwamishinan ‘yan sandan jihar Bolaji Salami ya tare Mataimakin Gwamnan yana kuma cewa  zai bari ya fita daga gidan gwamnatin jihar ba.

“Ka fice daga jam’iyar, an kawo min takardar ficewarka ofis” inji Kwamishinan ‘yan sandan a cikin bidiyon.

Sai mataimakin gwamnan ya kada baki ya ce ,”Idan ma na fice kai meye naka a ciki? Kwamishinan ‘yan sanda, ko kai ne shugaban jam’iyar APC ko PDP?

“Na yi iyakar kokarina wajen bin dokokin kasa domin kauce wa aukuwar rikici.

“Gwamna na amfani da kai wajen tauye min hakkina da tsarin mulkin kasa ya ba ni, na yi mamakin yadda dan sanda kamarka ya ba da kansa ana amfani da shi, ka bani kunya”.

“Mutanen jihar Ondo na sane da abin da kuke yi, ba za su yarda tarihi ya maimaita kansa ba, abin da ya faru a  1983 ba zai sake faruwa ba, ba za su lamunce maku ba, kai da mai gidanka”, inji mataimakin Gwamnan Ondo Agboola Ajayi yayin da yake mayar wa kwamishinan ‘yan sandan martani a cikin bidiyon.

%d bloggers like this: