Mataimakin Gwamnan Jihar Kwara kuma Shugaban Kwamitin Kwararru na yaki da COVID-19 a jihar, Kayode Alabi, ya warke bayan kamuwa da cutar.
Sanarwar da Mai Magana da Yawun kwamitin, Rafiu Ajakaye, ya fitar a safiyar Asabar ta ce gwaje-gwajen karshe da aka yi wa Mataimakin Gwamnan sun nuna babu kwayoyin cutar a jikinsa.
“Hakan ke nufin Mataimakin Gwama ya warke daga cutar kuma zai dawo bakin aikinsa”, inji shi.
- Waiwaye: Wata shida bayan bullar cutar coronavirus a Najeriya
- Mutum na uku ya rasu a hatsarin jirgi na Legas
Ya ce amma har yanzu iyalin Mataimakin Gwamnan na fama da cutar. “Gwamantin Jihar na wa matar Mataimakin Gwamnan da sauran masu fama cutar addu’ar samun lafiya”.
Sanarwar ta kara da gode wa mutanen jihar bisa addu’o’i da goyon bayansu da kuma ma’aikatan lafiya bisa sadaukar da kansu a yaki da cutar.
Ta kuma bukaci al’ummar jihar da su ci gabda da kiraye matakan da ake bi domin ganin bayan cutar a fadin Jihar.