✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matafiya sun kaurace wa hanya saboda na ce zan fito —El-Rufa’i

Gwamnar jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya ce an samu karancin motoci a kan iyakar Kaduna da Kano a ranar Juma’a da Asabar. Ya ce kila…

Gwamnar jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya ce an samu karancin motoci a kan iyakar Kaduna da Kano a ranar Juma’a da Asabar.

Ya ce kila hakan ya faru ne saboda bayyana aniyarsa da ya yi ta zuwa kan iyakar domin hana matafiya shigowa jihar domin hana yaduwar coronavirus.

Gwamna El-Rufa’i ya bayyana hakan ne ga manema labarai a kan iyakar Kaduna da Kano.

Ya ce ya fito kan iyakar jihohin biyu ne a ranar Juma’a da Asabar saboda cika alkawarin da ya yi.

“Na fito ne kamar yadda na yi alkawarin zuwa domin tabbatar da cewa mutane na bin doka yadda ya dace”, inji shi.

Game da ko ya gamsu da abin da ya gani sai ya ce, “Eh domin kusan duk motocin da na gani ban ga na fasinjoji ba duk tirerolin da na gani suna dauke ne da kayan abinci da aka amince a wuce da su.

‘Saboda zan fito ne…’

“Kila saboda na ce zan fito yau ne, sai duk masu san karya dokar suka kauracewa hanyar.

“[Ranar] Juma’a mun dauka wasu za su nemi karya dokar, amma hakan bai faru ba, shi ya sa na sake fitowa.

“Wasu jama’a ne ke son yada cutar – na ji dadin ganin cewa mutane na kula domin da ma abin da muke son gani ke nan,” inji shi.

Ya bayyana cewa an samu yawan mace-mace a wasu jihohi saboda gwamnoninsu ba su rufe iyakarsu ba wanda abin da jihar Kaduna ke gudu ke nan.

Ya ce gwamnatinsa na son samun goyon baya da hadin kan jama’a ne domin dakile yaduwar cutar cikin al’umma.