✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mata ta sheka wa mijinta tafasasshen ruwa a Kano

Matar ta ce aure dole aka yi mata da mijin nata.

Watar matar aure ta antaya wa mijinta tafasasshen ruwa saboda wata takaddama da suka samu tsakaninsu a garin Kano.

Magidancin da a halin yanzu yake a kokkone yana zaune tare da matar tasa ce a yankin Unguwa Uku.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.

Bayan an tsare ta sakamakon aika-aikan, matar mai shekara 17, ta ce da ma can sai da ta fada wa mahaifanta cewa ba ta son shi, amma suka yi mata auren dole da shi.

A cewarta, tun bayan daurin auren take ta fama da matsaloli a gidan nasa, ba kuma ya ciyar da ita, ballantana ta samu kulawar daga gare shi.