✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matar aure ta watsa wa mijinta tafasashshen ruwa

Wata matar aure ta zuba wa mijinta tafasashshen ruwa biyo bayan wata sa-in-sa da ta barke tsakaninsu. Maureen Miebode ta antaya wa mijin nata mai…

Wata matar aure ta zuba wa mijinta tafasashshen ruwa biyo bayan wata sa-in-sa da ta barke tsakaninsu.

Maureen Miebode ta antaya wa mijin nata mai suna Oyinkro Miebode ruwan ne a lokacin da ya ke tsaka da sharar barci.

Rahotanni sun nuna cewa aika-aikan da matar ta yi na da nasaba da rikicin da ya barke tsakaninsu a jajibirin ranar.

Yanzu haka dai Mr Miebode wanda mai matsakaitan shekaru ne na kwance yana jiyyar munanan raunukan da ya samu daga kunar.

Magidancin ya tabbatar da cewa rikicin ya fara ne bayan zargin da Maureeen ke masa cewa ya sa mata ido, abin da ya fusata shi har ya tsittsinka mata mari.

Ya ce ana gobe lamarin zai faru, sun yi da matar ta same shi a wajen aiki don ta karbi wayarta da misalin karfe 8:00 na dare, kwatsam sai ya gan ta da karfe 7:00 ta zo za ta wuce shi.

Ko da ya garzaya don ya ankarar da ita cewa yana tsaye yana jira sai ta rufe shi da masifa cewa me ya sa zai zo kafin lokacin da suka yi.

Ya ce, “Al’amarin nata ya daure min kai. Da na tambaye ta sai ta ce na sa mata ido. Ta ci gaba da zagi na muna kan hanya har muka isa gida. Na yi tunanin wutar za ta mutu iya nan amma ina.

“Da na fusata sai na marie ta har sau biyu na kuma umarce ta da ta tafi daki ta kwanta. Ana cikin haka ne wani abokina ya kira ni ya gayyace ni bikin zagayowar ranar haihuwarsa kuma ban dawo ba sai misalin karfe 1:00 na dare.

“Ina kwance kan doguwar kujera kawai sai ji na yi ta kwara min tafasashshen ruwan”, inji mai gidan.

Rahotanni sun ce tun lokacin da ta yi aika-aikar a garin na Yenagoa, matar ta yi layar zana, ko da yake dangin mijin sun ce ta kira waya da wata bakuwar lamba tana rokon ya yafe mata.

Yunkurinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Bayelsa ASP Asinim Butswat ya ci tura sakamakon kin daga wayar da ya yi da kuma rashin amsa rubutaccen sakon da muka tura masa.