Wata ’yar kasuwa mai suna Misis Ote Agbo, ta maka mijinta, Peter Ogah, a gaban wata kotun yanki da ke Nyanya a Abuja, bisa korarta daga gidansa.
Agbo, wadda ke zaune a yankin Karu a Abuja, ta yi wannan zargin ne a cikin karar da ta shigar a kan mijin nata.
- Ruftawar gada ta yi ajalin mutum 132 a Indiya
- Dubun mata da mijin da ke safarar mutane ta cika a Ogun
A cewarta, “Shekara biyu da suka wuce, na gano cewa mijina yana neman wata, lokacin da na tunkare shi da maganar, lamarin ya haifar mana da mummunan rikici a tsakaninmu.
Ta ce: “Hakan ta sa ya kore ni daga gidan da ni da yaronmu guda daya.”
Ta shaida wa kotun cewa a shekarar da ta gabata a lokacin bikin Ista bayan ta koma gidan saboda ’yan uwansa sun takura kan ta koma.
“Don haka a ranar Ista, na koma, lokacin da mijina ya gan ni, ya tambayi dalilin da ya sa na dawo, kuma ya sake kora ta a karo na biyu daga gidansa,” inji ta.
Don haka, ta roki kotu da ta raba auren nasu, sannan ta ba ta rainon dan nasu, sannan ta umarce mijin da ya rika biyan dukkan kudaden da suka dace don rainon yaron.
Sai dai wanda ake karar ya musanta dukkan zarge-zargen.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Labaran Gusau, ya dage sauraron karar har zuwa ranar 16 ga watan Nuwamba mai zuwa.