✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mata sun yi zanga-zangar neman a halasta karuwanci

Masu sana'ar na zargin ’yan sanda da kwace musu kudade da cin zarfinsu.

Mata sun gudanar da zanga-zangar neman hukumomi su halasta yin karuwanci tare da hana  ma’aikata kama masu sana’ar domin hukunta su.

Akalla mata masu zaman kansu 200 ne suka gudanar da zanga-zangar lumanar a ranar Alhamis a birnin Johannesburg da ke kasar Afirka ta Kudu; Wasu daga cikinsu sun rufe fuskokinsu, wasu kuma suka bari a bude.

“Da kudin karuwanci na saya wa kaina gida,” inji Constance Mathe, daya daga cikin masu zanga-zangar wadda ta ce ta shekara 16 tana sana’ar karuwanci.

Constance mai ’ya’ya biyu ta ce a baya ita ’yar aikin gida ce amma albashin da ake biyan ta na Dalar Amurka 72 a wata bai taka kara ya karya ba.

A yayin zanga-zangar da ta samu rakiyar ’yan sanda, Yonela Sinqu ta kungiyar SWEAT da ke kula da masu sana’ar ta ce ’yan sanda na musu barazana wajen karbe musu kudade da kuma cin zarafinsu.

“’Yan sanda na cin zarafinmu suna kwace mana kudade, sannan mata masu zaman kansu wadanda kwasotomi suka ci wa zarafi ba sa iya kai kara a ofishn ’yan sanda saboda su za a bige da yi wa shari’a saboda sana’ar tasu,” inji ta.

Kungiyoyin jinkai sun ce akalla mata 120,000 zuwa 180,000 ne ke sana’ar karuwanci a Afirka ta Kudu.

Dokar kasar ta haramta sana’ar, ta kuma tanadi hukunci ga masu yin ta da kuma kwastomominsu.

Dudu Dlamini, daya daga cikin matan da ke neman a halasta musu karuwancin, ta ce, “karuwanci sana’a ce ba aikata laifi ba.”

Dudu wadda take sanye da dan tofi da dogayen takalma ta shaida wa AFP cewar wadannan kaya take sanyawa zuwa wurin sana’arta wadda ta ce na bukatar kwarewa.