✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata sun yi gangamin yakar kashe-kashe a Zangon Kataf

Matan Hausawa, Fulani da Atyap Sun koka kan yadda ake kashe mazajensu

Matan Hausawa da Fulani da Atyap sun gudanar da zanga-zangar lumana don neman zaman lafiya a Zangon Kataf, Jihar Kaduna a yayin bikin zagayowar Ranar Mata ta Duniya.

Matan daga Karamar hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna sun gudanar da gangamain ne don bayyan takaicinsu kan ci gaban hare-hare a yankin Masarautar Atyap.

Wakiliyar matan Hausawa, Hajara Mohammed ta ce sun gaji da abubuwan da ake mana na cin mutunci da bata suna da kyama da [jin] haushin juna.

Ta ce, Idan ka kashe ni kai ba za ka mutu ba? In na kashe ki ni ba zan mutu ba?

Ina magana da babbar murya a madadin Kwamitin Matan Masarautar Atyap da kuma Hausawa na cikin garin Zango, Yau mun kawo karshe wannan alamari da yardar Allah.

Hajara ta koka cewa lamarin ya kai yadda “Maza su je su tsuguna a gona a sare musu wuya, [in] su bi hanya [kuma] a bi [su] a kekkashe su. In mazan sun kare ina matan za su?

Ta ci gaba da cewa, Mata mu gane wani abu; in an mutu an bar miki yara ya za ki yi da su?

Takwarorarta ta matan Fulanin, Hurera Ali da ta Atyap, Misis Rebecca Akut, duk sun yi tir da kashe-kashe da barnata dukiya da ake yi a masarautar tare da yin kira da a sake kawo karshen matsalar.

Da tale jawabi ga matan a garin Samaru Kataf ranar Litinin, jagoran gangamin, Misis Tabitha Yakubu Bako ta ce sun gaji da yadda ake kashe-kashe gaira ba dalili a masarautar.

Ta ce gangamin na su kuma roko ne ga mazajensu kan bukatar su daina fadace-fadacen domin a samu zaman lafiya tare da dakatar da yawaitar zawarawa da marayu da kashe-kashen ke haddasawa.

A sakonsa ga matan, Agwatyap, Sir Dominic Gambo Yahaya wanda Mista Luke Adankat ya wakilta ya yaba musu kan matukar damuwa da suka nuna kan munanan abubuwan da ke faruwa a masarautar Atyap.

Basaraken ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai an sami dawwamammen zaman lafiya a masarautar.

Shi ma a nasa jawabin, Shugaban kwamitin hadin gwiwar zaman lafiya da tsaro na Atyap, John Bala Gora ya jinjina wa matan ne saboda babbar shaawar da suke da ita na ganin cewa zaman lafiya ya dawo ga masarautar ta Atyap.