✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata su ne duniya!

Masana halayyar dan Adam da malaman addini da likitoci sun  yi ta kai- kawo da kokarin ganin sun fitar da bayanai na abin da suka…

Masana halayyar dan Adam da malaman addini da likitoci sun  yi ta kai- kawo da kokarin ganin sun fitar da bayanai na abin da suka fahimta daga iliminsu akan hikimar da Allah ke nufin bayyanawa a cikin bambancin jinsi da ke tsakanin mace da namiji, don fahimtar yanayinsu da kuma sanin irin rawar da kowannensu zai iya takawa a rayuwar mu ta yau da kullum.

Sun ce, “a tsarin halitta, idan muka dauki mafi girman jiki da tsawo; to namiji kenan, mafi yawan mata kananan jiki ne da su, kuma yawancin mata gajejjeru ne akan maza. Sautin muryar namiji tana da girma, ita kuma mace muryarta siririya ce.To mene ne abin mamaki don jin haka ga wanda ya san hikimar Allah da ke cikin yin hakan; watau da Allah Ya sa namiji da mace duk girma da tsawon su da sautin maganarsu daya ne, da ba wanda halittar daya za ta burgeshi, sai ma dai a rika gwabzuwa da juna idan aka samu bambamcin ra’ayi.

Mace ta fi namiji saurin girma,domin tun tana cikin mahaifa zuwa waje mace tafi yawan kwayoyin halittar garkuwar kamuwa da cututtuka.  Mace tana riga namiji saurin balaga, kuma tana riga namiji daina haihuwa. Idan muka kalli wannan gabar da kyau, wannanma kamar ta fassara kanta ne da kanta, tun da mace ta fi kwayar halittar garkuwar jiki ai ko za ta fi sauri girma ,tun da jikinta ba ya fuskantar wani kalubale mai yawa da zai tauye mata habakar  girmanta.

Shi ma saurin balagar ya samo asali ne daga bunkasar garkuwan jikinta ne, shi ya sa matan da ke cikin wadata da hutu su kan fi na karkara  saurin balaga, da dadewa cikin shekarun al’ada da kuma saurin fara al’adar.   Mace, shi ke sa kwayayen haihuwarta sukan riga na namiji saurin karewa.

Sai dai bincike ya nuna huhun namiji ya fi na mace zukar iska. Haka ma kwakwalwar namiji ta fi ta mace girma. Zuciyar namiji ta fi saurin bugawa akan ta mace. Shi ma wannan bambanci ya samo asali ne daga fifikon girman jikin na zahiri da na badini da namiji yake da shi fiye da na mace.

A halayya kuwa; masana sun yi ammana da cewa,namiji ya fi ta mace son aikin karfi, da gwagwarmaya, mace kuwa ta fi son tafiyar da komai a hankali cikin natsuwa.  A nan za mu iya gane cewa saboda  gabobinsa sun fi nata karfi ne, amma ita ma yanayin da aka yi ta na son yin komi a hankali cikin natsuwa ba illa ba ne a gare ta. Dalili kuwa shi ne, idan muka duba da kyau za mu iya gane cewa ita ce take da alhakin renon ciki da renon yara, za mu gane cewa hakan ne daidai da ita,domin da ta zama mai son yin aikin karfi da yin abu cikin gaggawa da cikin haihuwa bai zauna a jikinta ba,shi ya sa za ku ji a asibiti ana yi wa mata gargadin su daina yin aikin karfi ko aikin gaggawa idan suna da  juna  biyu, domin yin hakan zai iya haddasa musu yin bari.

Sannan kowa ya san yara sun fi son a rika tafiyar da lamarinsu a hankali, saboda su ma a hankali girma da wayonsu ke shigarsu, kuma mace ce mai renon su,don haka idan mun fahimci yanayi da take da shi, shi ma abin so ne ba nakasu ba ne.

Mace ba ta iya yanke shawara a gurguje,kamar yadda namiji kan yanke nan take. Eh,  kasancewar mace da wannan  dabi’ar shi ma wata baiwa ce a gareta ba wai nakasu ba ne, kamar yadda wasu maza ke gani. Domin idan muka duba muka ga aikin da take da shi na kula da iyali da gida da jama’ar gidan, za mu gane cewar lallai an yi hikima da aka halicce ta hakan, sabili da hakan ne ke ba ta dama ta dubi al’amurra,ta auna su ta gani kafin ta yanke hukuncin da ya dace,saboda ita ce ta fi sanin halin kowa a ckin iyali,kuma ta kan ji nauyinsu a kanta. Wannan dalilin ne ya sa da wuya ka ji an ce mace ta rataye kanta, ko ta kashe kanta.

Mace ta fi son kwalliya da duk wani abin da zai kayatar da ita da kuma son ta yi yanga fiye da namiji.  Haka ne domin ai ita aka halittawa kirar yin kwalliya da kayan yanga,irin su gashin kai mai tsawo da sauransu. da cika, aka hura kirjinta da mamuna, aka yi mata baya da kugu mai dauke da kira mai ma’ana, saboda Allah (SWT)Ya san ita abin sha’awa ce ga abokin jinsinta namij, to me ye nakasu gareta don tana dauke da ababen sha’awar da ke dauke hankalin namiji?

Da Allah bai yi wannan hikimar ba ya yaya za a samu bambancinta da namiji, kuma da ya za ta zama abin sha’awa da neman biyan bukata ga mijinta, har ya zama dalilin samar da zuriyya? Da kila sai dai mu zauna tamkar Mala’iku watau ba maza ba mata.

Haka nan mace ta fi namiji surutu, kuma ta fi namiji iya kula da harkar yara; ita a kullum hankalinta na akan cigaban iyali. Hakan kan faru ne a dalilin barinta gida da maza kan yi da iyali su tafi neman abinc, itace kullum suke tare da yara a gida cikin surutu da bari-bari,shi yasa ta kware a cikin yi musu hidima, kuma a  lura mace ko da yarinya ce za ka ga ta iya hidimar iyali, domin ita uwarta ke koyawa  ba ‘ya’yanta maza ba, don ta san ita ce za ta gajeta a gidan wani.

A takaice a game da dan bayanin da na gabatar a sama, za a iya gane wa mace ita ce sirrin zaman duniya.  Ita ce wacce uba da ’ya’ya suka dogara da ita wajen gudanar da harkokin gida da na yau da kullum a kodayaushe.

 

Za a iya samun A’isha Usman Liman ne a 09093467171