Hajiya Binta Muhammad ’Yanleman ta yi suna wajen taimaka wa mata da kananan yara a Hadeja da ke Jihar Jigawa. Yanzu haka ita ce Mataimakiyar Darakta a Ma’aikatar Kula da Kananan Hukumomi ta Jihar Jigawa. A zantawarta da Aminiya ta yi bayanin irin gwagwarmayar da ta sha a rayuwa da nasarorin da ta samu kamar haka:
Tarihina:
Sunana Binta Muhammad ’Yanleman da ke yankin Karamar Hukumar Kaugama a Masarautar Hadeja da ke Jihar Jigawa. An haife ni a 1964. Na fito ne daga gidan malamai domin a kasar Hausa idan aka cire gidan sarauta, to sai gidan malamai a daraja.
Alhamdulillah, zan iya cewa iyayena sun ba ni tarbiyya mai kyau, sun sanya ni a makaranta ta Islamiyya da ta boko inda yanzu haka nake cin gajiyarsu. Kakana yana daga cikin malaman da suka taso daga garin Futa Jallon na kasar Senegal zuwa Hadeja don yada Darikar Tijjaniyya. A kan haka ne ya sa ake yi wa gidanmu na ’Yanleman lakabin ’Yanleman Tijjanai, wato masu bin Darikar Tijjaniyya.
Na fara karatun firamare a garin ’Yanleman a 1969 daga baya aka mayar da ni firamare ta Shekara inda na gama a 1975.
Daga nan na wuce Kwalejin Horar da Malamai (WTC) da ke Gezawa kafin a raba jihohin Kano da Jigawa. Na kammala karatun sakandare ne a 1980.
Bayan na kammala sai na wuce makarantar Rano Rural inda na yi Diploma a 1983 da na kammala sai na ci gaba a dai a wannan makaranta inda na yi babbar Diploma wato HND inda na kammala a shekarar 2008.
Daga nan sai na wuce zuwa Jami’ar Bayero da ke Kano inda na yi digiri na gama a shekarar 2010. Haka kuma na yi digiri na biyu wato Masters a Jami’ar Bayero inda na kammala a shekarar 2011.
A halin yanzu ina da aure da da daya, kuma yana aikin dan sanda a Jihar Kano.
Aikin Gwamnati:
Maganar gaskiya na sha gwagwarmaya a aikin gwamnati. A lokacin da aka dauke ni aiki, an dauke ni ne saboda darajar mijina, domin a wancan lokaci an sanya dokar hana daukar ma’aikata aiki.
An dauke ni aiki ne a matakin albashi na biyar maimakon na bakwai. Haka dai na hakura na karba, yau ga shi abin ya zame mini alheri inda na kai matsayin Mataimakiyar Darakta.
Gaskiya na yi sa’a, domin wadanda suka koya mini aiki suna da tausayi, saboda tun ban iya komai ba, haka suka rika hakuri da ni har na koya. Amma a yanzu ba haka abin yake ba.
Matsaloli a lokacin aikin gwamnati:
Gaskiya ban taba fuskantar wata matsala a wajen aiki ba. Hasali ma ban taba samun matsala a bangaren mijina ko ’yan uwan mijina ba har zuwa yau. Domin tun farko na shaida maka cewa mijina ne ya samar mini aikin gwamnatin. Sai dai kalubalen da zan ce na fuskanta a yayin aikin gwamnati shi ne yadda a wancan lokacin babu mata masu yawa a bangaren aikin, hakan ya sa mu mata kalilan da ke aikin gwamnati ake yi mana wani irin kallo. Wadansu suna daukar mu a matsayin wadanda ba su da kamun kai, wadansu ma daukar mu suke a matsayin mata marasa tunani. A wancan lokaci babu wayewar kai, ba kamar yanzu ba da ilimi ya yalwatu, an samu ci gaba da wayewar kai inda ake samun mata masu yawa da ke yin aikin gwamnati. Ban da aikin gwamnati har siyasa mata ke shiga a wannan zamani saboda wayewar kai.
Kasashen da na ziyarta:
Duk da ban ziyarci kasashe da dama a rayuwa ba saboda ina da aure, amma na ziyarci kasashe kalilan. Sai dai wani abin sha’awa shi ne tare da maigidana muke yin tafiye-tafiyen, don a mafi yawan lokuta shi yake daukar nauyin tafiye-tafiyen don mu je ziyarar bude-ido ko ta yin ibada a kasar Saudiyya.
Daga cikin kasashen da muka ziyarta sun hada da Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar da Amurka da Sirilanka da kuma Saudiyya. don sauke farali.
Kasar da ta fi burge ni:
Ban da Saudiyya, babu kasar da ta fi burge ni irin Amurka. Don a Amurka akwai ’yanci kuma komai suna bi ne a ka’ida. Kasar ta yi suna wajen tsarin rayuwa musamman a bangaren kiwon lafiya, babu tsangwamar mutane, don ba ruwansu da addini ko kabilanci. A gaskiya na yaba da kasar Amurka.
Batun iyali:
Allah Ya albarkace ni da haihuwar da daya ne kawai a rayuwa. Namiji ne, kuma yanzu haka yana aiki ne dan sanda ne a Jihar Kano. Sai dai akwai ’ya’yan riko masu yawa da yanzu haka suke wajena.
Abincin da ya fi burge ni:
Gaskiya abincin da na fi sha’awa a kowane lokaci shi ne burabusko. Ba na gajiya da cin sa, da so samu ne, in rika cin sa a kullum. Ba na gajiya da cin burabusko musamman idan aka hada shi da miyar yauki.
Suturar da na fi so:
Na fi son atamfa musamman idan aka yi mata dinki na mutunci. Shi dinki irin na mutunci ko taro mutum zai shiga ba ya jin shakka.
Alakar gidanmu da Shehu Tijjani:
Eh, muna da alaka da Shehu Tijjani abin da ya sa ma ake yi wa gidanmu lakanin gidan Tijjaniyya ke nan. Kakana Malam Umaru Birom yana daga cikin malaman da suka kawo Tijjaniyya Masarautar Hadeja kimanin shekara 200 da suka wuce daga kasar Sudan. Hakan
ya sa ake yi wa gidan ’Yanleman da kirarin ’Yanleman Tijjaniyya.
Nau’in motar da na fi sha’awa:
Kirar Toyota irin ta zamani ta fi burge ni. Saboda ba ta shan man fetur da yawa, don idan ka zuba man Naira dubu uku daga Dutse za ta iya kai ka Hadeja kuma ta dawo da kai ba tare da wata matsala ba. A kan haka motar ke burge ni.
Kungiyoyi:
Ina da kungiyoyin da na mata da dama da na kafa a garin ’Yanleman don taimaka wa mata da kananan yara da kuma marasa galihu. Akwai wacce ake kira ’Yanleman Women Co-operatibe Society (BIM) da kuma wata da ake kira ’Yanleman Debelopment Initiatibe, kuma dukansu suna yin aiki kafada-da-kafada ne don taimaka wa al’ummar ’Yanleman.
Abin da ya fi bata min rai:
Gaskiya babu abin da ya fi bata mini rai irin yadda ake yawan yi wa mata da kananan yara fyade a wannan zamani. Ba zan manta ba akwai lokacin da wani tsoho ya yi wa wata karamar yarinya fyade a lokacin da aka kira kungiyarmu ta IMWON a matsayina ta Sakatariyar Kungiyar, a lokacin da muke yi mata wasu tambayoyi abin ya ba ni haushi da tausayi, domin an bata rayuwar yarinyar da ba ta san komai a rayuwa ba.
Sakona ga mata:
Mata ku tashi ku nemi ilimi, domin ilimi na gaba da komai a rayuwa. Idan aka ce ilimi, ina nufin ilimin addini da na zamani. Idan mace tana da ilimi, za a rika damawa da ita a rayuwa a kowane fanni, musamman a aikin gwamnati da bangaren siyasa ko kasuwanci. Sannan mace mai ilimi ta fi wacce ba ta da ilimi daraja, ko a rayuwar aure ne.
Sannan in kira ga iyaye su guji dora wa ’ya’yansu musamman mata talla, don talla wata jami’a ce ta lalata tarbiyya. Idan suka tarbiyyantar da ’ya’yansu, za su ci gajiyarsu a lokacin da suke raye da kuma bayan rayuwarsu.