Wata kungiyar mata Musulmai ta kafa gidan rainon marayu a birnin tarayya, Abuja.
Kungiyar ta ce gidan mai suna ‘Halal Children’s Home II’ zai kuma kula da yara da masu karamin karfi domin kawar da su daga kan tituna da ba su tarbiyar da ta dace.
- An kara sako dalibin Jami’ar Greenfield
- An kori kwamandan Hisbah da aka kama da matar aure a otal
- Ba kowane irin fim nake shiga ba — Tijjani Faraga
Shugaban Kunigiyar, Ramatu Abubakar, ta ce a halin yanzu marayu 70 ne gidan ya fara kula da su.
Da take magana a taron kaddamar da gidan marayun, Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen, ta bukaci ’yan Najeriya mawadata da Allah bai ba wa haihuwa ba da su rika zuwa suka daukar marayu domin kula da su ta hanyar da ta dace.
Pauline Tallen ta ce yawacin yaran da ke tasowa babu cikakkiyar kulawa ne ake wayan gari sun fitini al’umma, shi ya sa yake da muhimmanci a rika bayar da gudunmuwa wurin daukar nauyinsu da tarbiyantar da su.
Shi ma wani magoyin bayan kungiyar mata Musulmin, Vice Admiral Jubrila Ayinla (mai ritaya), ya jaddada muhimmancin ilimantar da kananan yara, tare da bayyana kwarin gwiwar cewa gidan marayun zai kyautata rayuwa kananan yaran.
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Mbora da ke Rukuncin Gidajen Citec, Ustaz-Musa Muhammed, ya ce masu kula da marayu na da babbar lada a ranan gobe Kiyama.
Shugaban Kunigiyar, Ramatu Abubakar, ta ce a halin yanzu marayu 70 gidan ke kula da su.