Hajiya Fatima Usman Alto kwararriya ce a fannin zamantakewar al’umma kuma darakta ce a bangaren mulki da tsare-tsare a offishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, a zantawar da Aminiya ta yi da ita, ta yi tsokaci bisa fadi-tashin da mata kan shiga a rayuwa, ta kuma bayyana hanyoyin magance matsalar da mata kan fuskanta ta hanyar ba su ilimi da sana’a.
Aminiya: Za mu so ji takaitaccen tarihinki?
Sunana Fatima Usman Alto, kuma idan ina maganar tarihina, sai na tabo kananan hukumomi uku. Ka ga dai asalin iyayena mutanen danbatta ne a Jihar Kano, sannan asalin gidansu mahaifina na cikin birnin Kano ne a unguwar Danbazau wato karamar hukumar Dala, sannan asalin inda aka haife ni a Gwangwazo ne karamar Hukumar Municipal. Na yi makarantun firamare a gidan sarki a makarantar gidan makama kurmawa, daga nan na tafi makarantar sakandare ta ‘yan mata ta Dala a shekarar 1975, na je makarantar share fagen shiga Jami’a ta CAS da ke Kano, kafin daga bisani na wuce Jami’ar Bayero ta Kano a shekarar 1983, inda na yi karatun digirin farko a fannin sanin zamantakewar al’umma. Ina karatu a jami’ar ne na yi aure da ma’aikacin jarida. Allah Ya albarkace mu da ‘ya daya. Bayan karatuna na kama aiki da ofishin shugaban ma’aikata na Jihar Kano a shekarar 1988, tun a wancan lokacin na samu matsayi daban-daban a yanzu ina matsayin daraktan mulki da tsare-tsare.
Aminiya: Kina karatu sai aka yi miki aure, ko ya aka yi ki ka hada karatu da aure?
Haka na hada su duk da wahalhalun da suke tattare da yin haka domin a lokacin har reno nake, amma na samu karfin guiwar jajircewa kan karatuna wajen iyayena da shawarwarin da suka yi ta ba ni, sun kuma taimake ni kwarai wajen renon ‘yata domin da na yi auren ma ban bar unguwarmu ba.
Aminiya: Me zaki ce game da muhimmancin ilimi ga ’ya mace?
Akwai alfanu a ilimin ’ya’ya mata kwarai da gaske, ai ita mace abu hudu ce ke da amfani a rayuwarta, farko tasan addininta sanin addinin shi zai tallafa mata tasan muhimmancin kanta ta nemi ilimi wato ilimin addinin da na zamani samun ilimin shi zai tallafa mata wajen tunanin samar da iyali, addininta da iliminta su za su sa ta samu lafiyayyen iyali ingantacce abin alfahari a al’umma saboda dabi’u da al’amuran iyalinta wajen yin mu’amala da sauran jama’a za ka ga ya bambanta komai za ka ga cikin nutsuwa da sanin ya kamata za su dinga tafiyar da harkokinsu na rayuwa, cikon na hudun kuwa shi ne ya zamanto tana da sana’ar yi ba lalle sai ta fito waje don yin sana’a ba. Akwai sana’o’in da za ta iya aiwatarwa a cikin gidanta wanda zai tallafa mata wajen samun karin rufin asiri na hidimomin rayuwa shi ma zai sa karin nutsuwa ga iyalinta har ma ta taimakawa al’umma. Ka ga ilimin mace tamkar taimakawa al’umma ne.
Aminiya: Ko akwai kiran da za ki yiwa iyaye kan kula da ilimin ’ya’ya mata?
Iyaye maza ya kamata ku kula da bawa matayenku ilimi wato ilimin zamani da na addini domin duk suna da muhimmanci a rayuwar mace wanda kai da kake kusa da ita zaka fi kowa samun alfanunsu, ka ga idan ka taimaka mata wajen ilimi amfani kanka ne ko da wajen koyawa da dorawa yara darasin da aka koya musu a makaranta ne. Iyalin da suke da ’ya’ya maza da mata bance su fito fili su nuna baiwa ’ya’yan su mata goyon baya ba fiye da maza amma ta hikima idan suka fifita baiwa ’ya’ya mata zai hassasa abubuwa da yawa a rayuwar ’ya mace wanda za a ga alfanun su idan aka dorata kan sanin muhimmancin ilimi zata ginu a kai harma ta jawo hankalin saura ’yan uwanta maza.
Aminiya: Ko akwai wani kalubale da kika fuskatan yayin karatun ki da aiki kasancewar ki ’ya mace?
Kusan yawancin al’amura na rayuwa ba a rasa kalubale, kalubalen da na cikaro da shi a lokacin karatuna shi ne mijina baya son karatun, ya so ya hana ni amma sakamakon goyon bayan da na samu daga mahaifina sai Allah Ya taimake ni ya amince.
A wajen aiki kuwa babban kaluballen da mata kan fuskanta shi ne rashin fahimta abubuwan da kake so ka aiwatar ko ka riga ka aiwatar ko da abin nan mutum shi zai amfana, sai ka ga baya so, kuma ba sa fahimta, wani lokacin ba son ranmu ba ne a yanayin aikin ne ya zo da haka. Tun da mu yanayin aikinmu yana da shimfidaddun ka’idoji da kasidun tsarin aiki da ma’aikaci ya kamata a ce ya sani kuma yana amfani da su, inda ya dace. Misali kowane laifi a aikace yana da hukuncin da ya dace da shi, wani lokacin mutane a aikace suna yin laifin wanda su ba su sani ba ko kuma ba sa son. Kuma ka ce musu a dokar aiki laifi ne, yawancin mazajenmu Hausawa ba sa son yin aiki da mata, sai su dinga danganta aikin mata da cewa akwai rauni, wanda ba haka ba ne aikin da wasu matan za su aiwatar ya zarta na wasu mazan da yawa. Sannan maza ba su cika tallafawa mata ba, wajen aiki, a da ne ake samun haka har ka ga namiji na ba mace shawarar ga wani karin bayani ki kara a aikin ki don ya inganta.
Wata babbar rashin fahimtar sai ka ga tsakanin ma’aikata mata ba a jituwa, wadannan kadan ne daga cikin kalubalen da na fuskanta.
Aminiya: Ko mene ne sakon ki ga mata baki daya?
Sakona ga mata shi ne duk abin da za mu yi ya zamananto muna dubawa, muna hangawa ta kowane bangare mu yi nazari sosai kafin yanke hukunci ko aiwatar da wani kudiri. Mu ne ya kamata a ce muna da kaifin tunani saboda mace, ke ce matar wani ke ce uwar wasu ’ya’ya (maza da mata), sannan ke ce ’yar wasu wato iyayenki ke nan don haka kun ga ke nan mata sun tabbata iyayen giji, wadanda aka sansu da dattaku da kamala. Sabanin irin abin da ke faruwa a yanzu yadda wasu mata cikin jahilci ke tafka aika-aika. Abin bakin ciki za ka ga hatta yara kanana wadanda ba su ji ba, ba su gani ba suna fadawa cikin hadari na muggan dabi’un ire-iren wadannan jahilan matan.
A baya-bayan nan ne a Jihar Kano wasu mata suka karya wani dan karamin yaro, suka nakasa shi, sai gashi kuma a Jihar Neja wata mata ta yanke al’aurar dan kishiyarta irin wadannan aiki ne na jahilci duk macen da aka bai wa ilimi ba za a same ta da wannan ba.
Mata mu rungumi ilimi da sana’a – Hajiya Fatima