✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata mu nemi ilimin addini da na boko don jin dadin rayuwa –Dokta Fatima Musa

Dokta Fatima Binta Muusa ita ce shuugabar Kwalejin mata ta Gwamnati da ke Jihar Sakkwato, watau GGC, ta shahara a fanin da’awa da taimaka wa…

Dokta Fatima Binta Muusa ita ce shuugabar Kwalejin mata ta Gwamnati da ke Jihar Sakkwato, watau GGC, ta shahara a fanin da’awa da taimaka wa mata a jihar Sakkwato.   Mace ce da ake yaba kwazonta da jajircewarta a kan ganin ta cimma burin da ta sanya a gaba. Aminiya ta tattauna da ita kan tarihin rayuwarta da kuma shawarwarinta ga mata da sauran abubuwan da suka shafi matan. Ga hirar kamar haka:

Tarihinta
Bismillahir RahamanirRahim.  Sunana Hajiya Fatima Binta Musa. A Jihar Sakkwato aka haife ni. Kuma rayuwata gaba daya nan na aiwatar da ita ne a Jihar Sakkwato.  Na yi makarantar firamare  a makarantar Muhammad Bankanu da na kammala sai na wuce makarantar mata ta Bodinga na yi shekara uku, sai na wuce babbar sakandaren ’yan mata ta Kangiwa na yi aji hudu zuwa shida a nan na samu nasarar jarabbawa mai daraja ta biyu watau Grade II.  Daga nan na nemi gurbin karo karatu a  Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato na yi kwas na fara share fagen karatun digiri na shekara daya, bayan na kammala ne aka ba ni gurbin karatun  digiri a bangaren ilmin Musulunci waton Islamic Education. Bayan na gana sai na yi bautar kasa (NYSC) a Jihar Ondo amma ban kammala ba sai aka mayar dani Talatar Mafara don a can ne mijina yake aiki da Rima Basin sai na karasa a can. Na shekara biyu da kammala karatuna bana aikin gwamnati don a lokacin mijina bayason aikin gwamnati ga ‘ya mace daga baya ne abokansa suka nuna masa amfanin aikin ko karantarwa ne, ya yarda da shawararsu amma sai ya sanya min sharaddn zan yi karantarwa ne kurum a makarantun mata zalla.  Daga nan sai na fara koyarwa a  makarantar mata ta Mafara a matsayin malama.   Na zauna can har na zama mataimakiyar shugabar makaranta, bayan wancan lokcin muka yi hargitsi kan masallaci tsakanin MSS da shugabbar a lokacin ina tare da MSS, sai aka raba mu inda aka mayar da ni makarantar mata da maza ta Arkilla a nan na zauna ina neman canjin makarata har na samu.   Ban taba shiga aji ba don kiyaye ka’idar mijina ta ba zan karantar da maza ba, daga nan aka mayar da ni makarantar Hafsatu Ahmadu Bello a matsayin malama.  A wannan makaratar na sake zama mataimakiyar shugaba na wani lokaci daga nan sai na samu kiran Kwamishiniyar ilmi ta wancan lokaci Hajiya Kulu na tafi ofishinta, sai ta gaya min an yi min karin girma na zama shugabar makarantar mata ta Rabah.   Bayan shekara daya sai ta mayar da ni karamar Hukumar Ilela na yi shekara uku, daga nan aka sake dauke ni zuwa makarantar mata ta Tambuwal na yi shekara bakwai daga nan aka mayar da ni wannan makaratar mata ta Jihar Sakkwato watau Gobernment Girls College ( GGC).  Bayan na kammala sai malakmina Farfesa Malami Tambuwal ya ba ni shawarar na cigaba da yin digiri na uku watau Dokta. Da farko kamar ba zan yi ba, amma da na daure sai ga shi yanzu na zama Dokta a fannin ilimi.

Shawararta ga mata
Su yi hakuri a gidaen mazajensu musamman wadanda ke tare da abokan zama ma’ana matan da  mazajensu suke  tare da wasu don duk yadda mace ta kai ga yin kishi ba za ta iya sanya miji ya rabu da kishiyarta ba sai Allah Ya kaddara.  Kuma hasalima shi zama aure ai ibada ne, sai mace ta ki ji kuma ta ki gani idan tana son cin ribar rayuwa.  karin Shawara ta ga mata shi ne lokaci ya yi da za a yi karatun addini da na zamani.  Duk macen da ta yi karatun addini ba ta yi na boko ba rayuwarta ba daya ba ce da wadda ta yi karatun boko da na addini da kuma wacce ba ta yi karatun kwata-kwata ba. Sannan ina ba mata shawara su rungumi sana’a bayan sun yi ilimi.  Mace ko a cikin gidanta za ta iya yin sana’a irin su dinki ko yin fanke da sauran kananan sana’o’i.  Sai dai a rika jin tsoron Allah a duk abin da mace take yi, idan aka samu haka to Allah Zai ba mu mafita.

Abbubbuwan da kike ganin suna yi wa mata tarnaki a wannan zamani
Gaskiya bai fi rashin tsoron Allah da kishi ba.  Babu wanda zai hana mace yin

kishi amma dai za ki yi shi ne tsaka-tsaki.  Dole mace sai ta hada da yin hakuri a zamantakewar aure.  Don Hausawa kan ce hakuri shi ne maganin zaman duniya.
A wannan zamani da muke ciki ana fadin mata ba sa yin karatu ya za ki kwatanta karatunsu a yanzu da kike shugabar makaranta da lokacin da kike daliba?
Gaskiya magana ita ce ba a yin karatu a da kamar yanzu.  Kuma mutanen birni sun fi yin karatu a kan na kauye.  Idan kana birni za ka ga mutanen birni suna karatu don su ne ke gama sakandare su tafi ta gaba da ita a manyan makarantu da jami’o’i amma in ka  auna yawan matan birni da na karkara za ka  gano ba sa yi, matan karkara in an yi kokari ne iyayensu ke bari su kammala sakandare, wata ma ba ta gama wa ake cireta a yi mata aure.   Da wannan nake cewa gaskiya muuna bukatar mata su tashi zuwa karatu musamman na kauyukka inda ba a karatu mai yawa.

kungiyar data ke ciki na mata
Ina cikin kungiyar ‘yan uwa mata  (MSO), na taba yi masu sakatariya na kuma zama Amira yanzu ni ce amira shura ta wurinsu. Ita kadai nake ciki don kungiya daya nake yi duk da tana a karkashin kunggiyar mata musulmi ta kasa (FOMWAN). Mun samu nasarori da dama a kungiyarmu in da muke shirya taron ilmantar da mata a wata-wata wanda ake kira mu’utamar.   Malamai ne ke zuwa su yi wa’azi a fannoni  dabban-dabban, sannan muna shirya taro na shekara-shekara shi ma wanda muke tara dukkan ‘yan mata dake makaratun sakandare na jiha mu fadakar da su abin da yake daidai da wanda yake kuskure, don in sun koma gida su karantar da wasu halayya nagari.   Mun bude Islamiyoyi a kauyukka da yawa, cikinmu ne ake
samun masu zuwa karantar da mutane a kauyukkan don mun fahimci akwai matsalolin jahilci ga matan karkara, abin sha’awa a nan ba mu neman taimako wajen kowa sai wanda ya ga dama ya ba mu don mafiyawancinmu ma’aikata ne da ‘yan kasuwa mata.   Mukan tara kudin wata-watadon gudanar da ayyukanmu  don da ma  ayyukkanmu na gudanar da wa’azi ne.

Suturar da tafi burgeki
Hijabi dogo har kasa

Bambancin rayyuwar mata a makaranta da kuma gida
A matsayina na daddiyar shugabar makaratun mata, zan gaya maka gaskiya ba wani bambanci duk rayuwar da yarinya take yi a gida haka ma zai kasance a makaranta in baicin tsafta, don duk yadda ka ga yarinya a gida kazama a makaranta za ka ganta tsaf.   Yadda  abokai ke bata tarbiyya ko gyara yarinya a gida, ko a makaranta haka abin yake.  Halayya da dabi’ar mata iri daya ce a duk in da su ke.   Kirana kawai iyaye su kula da tarbbiyar yaransu mata a kodayaushe su san in da suke zuwa da dukkan wadanda suke yin hulda da su don gudun kada kana saka wani kuma yana warware maka.

Hada aikin gida da karantarwa
Hada aikin gida da karantarwa bai ba ni wata wahala ba sosai.  Allah Ya hada ni zama da abokiyar zama ta arziki mai hakuri da sanin ya kamata.  Duk wani aiki da yakamata na yi kamar shirya yara zuwa makaranta da kula da yara da aikin gida, da zarar ina wurin aiki ita ke yi.   Ina alfahari da wannan abokiyar zamana, Allah Ya kara hada kanmu da abokiyar zamana da miinmu mai fahimta da hakuri watau Malam Lawal Maidoki.
Wallahi da mata za su samu irin abokiyar zamana da mijina da sun huta kamar yadda Allah ya albarkace ni da samun wannan cigaban.