Hajiya Halima Diko ’yar asalin Birnin Kebbi ne fadar Jihar Kebbi. Tsohuwar malamar makaranta ce, yanzu kuma Babbar Sakatariya ce a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kebbi. Mai son ci gaban talakawa ce, musamman a bangaren samun ingantaccen ilimi. Ta bayyana wa Aminiya tarihinta da gwagwarmayar da ta sha:
Tarihin rayuwata:
Sunana Hajiya Halima Diko ni ’yar asalin Jihar Kebbi ce kuma an haife ni a garin Birnin Kebbi. Na fara neman ilimi da makarantar allo a makarantar Malam Na-Abu Liman a garin Birnin Kebbi daga nan na shiga Santaral Firamare a 1977, na fara da rabin aji daga nan sai wata ’yar uwata da ke aure a garin Zuru ta dauke ni ta tafi da ni Zuru.
A Zuru na fara firamare a Makarantar Sami Gomo da aji daya da ma tun daga Birnin Kebbi na gama rabin aji. Bayan ina nan a Zuru na kai aji uku sai aka tafi da ni Legas na yi shekara biyu daga nan aka dawo da ni Birnin Kebbi inda na karkare firamare a makarantar Makerar Gandu wadda ake kira Atiku Bagudu Sakandare a yanzu a nan na yi aji shida zuwa bakwai.
Bayan na gama sai na ci jarrabawar zuwa Kwalejin ’Yan mata (GGC) da ke Sakkwato a 1982.
Bayan na gama sakandare sai na wuce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na yi karatun share fagen shiga jami’a, sannan na ci gaba a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato bayan na shekara daya a Zariya saboda a lokacin za a yi mini aure. A nan Usman Dan Fodiyo na yi digiri na farko. Bayan na gama sai na yi hidimar kasa a Makarantar Mata ta (Nana Girls) da ke Sakkwato.
Bayan da na gama hidimar kasa na dawo gida, sai na samu aikin koyarwa inda aka tura ni Makarantar Sakandare ta Giginya da ke Sakkwato, ina nan ban ko shekara biyu ba sai na samu aiki a Jami’ar Usman Dan Fodiyo a ofishin rajistara (Magatakarda). Ina Sakkwato a 1991 aka kirkiro Jihar Kebbi sai na dawo gida na kama aiki a Makarantar Kimiyya da Kere-Kere ta Birnin Kebbi, wato Waziri Umaru Federal Polytechnic, a1992 na koma aiki a karkashin jiha inda na fara aiki a Hukumar Fansho ta Kananan Hukumomi. Daga nan sai aka canja ni zuwa Hukumar Fansho ta Malaman Firamare. Ni ce na bude wannan hukuma, inda na shekara goma a hukumar.
Ina wannan hukuma har zuwa shekarar 2016 inda Mai girma Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya nada ni Babbar Sakatariya, aka tura ni Ma’aikatar Mata ta Jihar Kebbi. Bayan na yi watanni sai aka canja ni zuwa Ma’aikatar Kiwon Lafiya inda nake har yanzu, yanzu shekara biyu ke nan ina rike wannan mukami.
Kalubale:
Kalubale da zan ce na samu shi ne kamar aikin da na yi a Jami’ar Usman Dan Fodiyo, domin wuri ne da masu ilimi da tunani da sanin ya kamata suke, duk abin da mutum zai yi sai ya samu wani ya yi masa gyara, dole duk abin da za ka yi sai ka natsu saboda duk wanda za ka yi hulda da shi malami ne ko dalibi sai ka kwantar da hankalinka, kuma ka rika tunanin wanda kake hulda da shi, domin mai zurfin ilimi da tunani ya san inda duniya ta nufa. Wanda duk ya yi aiki a irin wadannan wurare dole ya rika samun kalubale, amma kuma za ka goge.
Burina:
Shi ne in ga na gama aikin gwamnati lafiya, kuma idan mutuwa ta zo in cika da imani. Domin babu wani buri ga ma’aikacin gwamnati illa ya kai matsayin Babban Sakatare ya kuma gama aiki gwmnati lafiya.
Tarbiyya daga iyaye:
A gaskiya iyayena sai dai in ci gaba da yi musu addu’ar Allah Ya saka musu da alheri. Domin a kullum suna yi mini huduba cewa duk inda nake in zama mai hakuri, kuma duk yadda na ga mutum in mutunta shi in ya girme ni in ba shi girman da Allah Ya ba shi. Sukan ce mini kada in zama mai wulakanta jama’a a duk irin mukamin da na samu kuma in rika daraja mutum babba ko karami. A kan haka ne duk ma’aikatar da na je za ka ga ina mu’amala da jama’a kuma da zarar an canja ni daga wannan ma’aikata za ka ga jama’ar da muke aiki da su ransu yana baci. Ba komai ne ya jawo mini haka ba illa tarbiyyar iyaye da na dauka tun ina karama.
Kasashen da na je:
Na je Amurka da Saudiyya da Habasha da Tanzaniya da Nijar da Ghana.
Haduwa da maigida:
Maigidana aminin yayana ne, ta nan ne muka hadu domin yana zuwa wajensa. A haka ne ya gan ni ya ce yana sona har Allah Ya hada mu muka yi aure, yanzu muna da ’ya’ya shida maza uku mata uku, kuma dukansu suna nan.
Shawara ga mata:
Shawarata ga mata ita ce su dage wajen neman ilimin addini da na zamani musamman na addini don sai kin samu ilimin addini kafin ki san muhimmancin samun na zamani. Idan mace tana da ilimi ba shakka za ta taimaka wa mai gidanta ta hanyoyi da dama.
Kuma ita kamar malama ce ga ’ya’yanta. Saboda haka dole ne ta nemi ilimi kafin ta iya koya wa yaranta tarbiyya. Kuma iyaye mata su rika matsa wa mazansu wajen sanya ’ya’yansu a makaranta domin tarbiyyantar da rayuwarsu, haka su ma ’yan mata wadanda suke makaranta su kauce wa bai wa malamai kudi ko kansu domin su ci jarrabawa, wannan ba karamar illa ba ce, kuma in kin yi haka kin cuci kanki da iyayenki da kasa baki daya.